Sagir Abubakar" />

Barnar ‘Yan Bindiga: Buratai Ya Jajanta Wa Katsinawa

Shugaban rundunar sojan kasa, laftana janar Tukur Yusuf Buratai, ya jajanta wa Sarkin Ruman Katsina, Hakimin Batsari da al’ummar karamar hukumar bisa harin da ‘yan bindiga suka kai kwanan nan a yankin.

Buratai, wanda ya samu wakilcin jami’i mai kula da ba da horo da aikace-aikace, Manjo Janar Lamidi Adeosun, a lokacin ziyarar jajantawar.

Ya ce, tawagar ta zo jihar Katsina ne domin tantance matakin nasarorin da aka kammala ya zuwa yanzu wajen yaki da hareiharen ‘yan bindiga.

Ya ce, Shugaban rundunar sojan kasa, ya nuna damuwa bisa abin da ya faru, inda ya tabbatarwa al’ummar yankin da na jiha cewa, za a ci gaba da yin kokari wajen shawo kan matsalolin tsaro da ake fuskanta a yankin.

Kamar yanda ya ce, rundunar sojan Nijeriya ta canzawa kwamandan brigade ta 17 da ke Katsina wurin aiki, inda ta musanya shi da wani.

Ya bukaci al’umma a koda-yaushe su rika taimaka ma jami’an soji da muhimman bayanai a kan maboyar ‘yan bindigar.

Ya ce, tuni shugaba Muhammadu Buhari, ya ba da muhimman kayayyakin aiki da za su taimaka wajen tunkarar ‘yan ta’addan.

Tukur Burtai, ya yaba ma goyon bayan da karamar hukumar hakimin yankin da kuma al’ummar yankin ke ba da wa wajen kawo karshen aikace-aikacen ‘yan bindigar a yankin.

Da yake jawabi, shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Batsari, Alh. Mannir Mu’azu Rumah, ya ce al’ummar yankin yanzu za su samu natsuwa tunda jami’an sojin za su iya tunkarar ‘yan ta’addar.

Ya bukaci al’ummar da su ba jami’an tsaron hadin kai da goyon baya wajen samun nasarar gudanar da ayyukansu wajen kawo karshen kalubalen tsaro a yankin.

A jawabin godiya, Sarkin Ruman Katsina, Alh. Tukur Mu’azu, ya bayyana godiyarsa ga shugaban rundunar sojin bisa ga ziyarar inda ya yi kira da a kara tura jami’an tsaro ga al’ummar yankin.

Ya yi kira ga al’ummar yankin da su tona asirin duk wani mutum da ke da alaka da ‘yan bindiga ga jami’an tsaro.

Wakilin shugaban rundunar sojin ya sha ruwa da jami’an sojin da ke sansanin na Batsari inda suka ci abinci, a wani bangare na bukukuwan karamar sallah da kuma samun cikakkiyar nasarar kammala azumin Ramadan.

Exit mobile version