Arewa Maso Yamma Na Da Dalibai 157,831, Arewa Maso Gabas 127,058, Kudu Maso Yamma 92,850, Arewa Ta Tsakiya 74,120, Kudu Maso Kudu 37,180, Kudu Maso Gabas 27,098
Hukumar Bayar da Lamunin Karatu ta Nijeriya (NELFund), ya raba jimillar kudade kimanin Naira biliyan 99.5 ga dalibai da cibiyoyin ilimi a cikin wata 16 kacal, tun bayan kaddamar da shirin bayar da rancen a ranar 24 ga Mayun 2024.
- Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin
- Xi Ya Taya Jami’ar Tianjin Murnar Cika Shekaru 130 Da Kafuwa
Dangane da bayanan hukumar da LEADERSHIP ta samu daga rahoton matsayin rarraba lamunin daliban, wanda ke dauke da kwanan watan 24 ga Satumbar 2025, dalibai kimanin 510,378 ne ya zuwa yanzu suka ci gajiyar shirin bayar da rancen.
Kasafin ya nuna cewa, an biya Naira biliyan 53.8 ne kai tsaye ga cibiyoyi ko makarantu a matsayin kudin karatu, yayin kuma da aka biya daliban Naira biliyan 45.7 a matsayin alawus-alawus.
Don haka, a dunkule dai; kimanin makarantu 228 ne ke cikin wannan tsari a halin yanzu a dukkanin fadin wannan kasa.
Bayanan sun bayyana cewa; “Jimillar makarantu 228 suka ci gajiyar shirin, inda kimanin dalibai 829,423 suka nema. Ya zuwa yanzu kuma, dalibai 510,378 ne suka samu wannan tallafi na bayar da rance.
“Zuwa 10 ga watan Satumba, an biya kimanin Naira 53,801,717,293.00 a matsayin kudaden makaranta na daliban, yayin kuma da aka biya Naira 45,751,360,000.00 a matsayin alawus-alawus na daliban. Idan aka tattara kudaden baki-daya, jimillarsu ta kama Naira 99,553,077,293.00,” a cewar rahoton.
Duk da nasarar da aka samu a fadin kasar, shirin ya fuskanci kalubale wajen ganin an yi adalci a rabon a dukkanin shiyoyin fadin kasar guda shida da ake da su.
Alkaluman da LEADERSHIP ta tattara a watan Mayun 2025, sun nuna dimbin gibin da ke tsakanin Arewa da sauran yankunan fadin wannan kasa.
Arewa Maso Yamma, ta samu mafi yawan masu neman karatu da dalibai 157,831, sai kuma Arewa Maso Gabas da 127,058, haka nan kuma Kudu Maso Yamma da 92,850.
Akasin haka, dalibai 27,098 ne kadai daga Kudu Maso Gabas da kuma 37,180 daga Kudu Maso Kudu, yayin da Arewa ta Tsakiya ke da 74,120 da suka nema.
Yayin da aka yi kokarin jin karin bayani a kan rashin daidaiton da aka samu a fadin sassan kasar, Madam Oseyemi Oluwatuyi, Daraktar Sadarwa a Hukumar Bayar da Lamunin Karatu ta Nijeriya (NELFund), har yanzu ta ki cewa uffan, inda kadai ta ce; “A yi hakuri, ba za mu iya ba da irin wadannan bayanan ba, domin suna da matukar muhimmanci.”
Babu shakka, wadannan alkaluma; sun haifar da cece-kuce da kuma mabanbantan ra’ayoyi a tsakanin masu ruwa tsaki a harkar ilimi da kuma shugabannin yankuna.
Da yake zantawa da daya daga cikin wakilanmu, Mista Isaac Oche, masanin kididdiga da ke Abuja ya ce; karancin neman tallafin daga Jihohin Kudu Maso Gabas kamar yadda Hukumar Asusun Bayar da Lamunin Karatu ta Nijeriya (NELFund) ta rawaito a baya, na iya kasancewa ne sakamakon fargabar da daliban ke yin a gudun kada basussuka su yi musu yawa.
“Yawan adadin yana nuna cewa, dalibai daga Kudu bas u cika cin gajiyar wannan shiri ba, duk da cewa; na san Hukumar NELFUND, ta yi matukar taka-tsan-tsan a yankin, sannan kuma na yi imanin cewa; an samu ci gaba idan aka la’akari da halin da aka samu a halin yanzu,” in ji shi.
“Haka kuma, tana iya yiwuwa saboda rashin yarda da tsare-tsaren gwamnati ko kuma rashin sanin ya kamata tun daga tushe. Don haka, akwai bukatar wayar da kan jama’a na wannan yanki, sannan kuma ina yaba wa hukumar; bisa matukar kokarin da suka yi, amma har yanzu akwai bukatar a kara kaimi, domin kawar da shakku tare da aiwatar da gaskiya.”
A nasu bangaren, daliban sun yaba da shirin a matsayin daya daga cikin manufofin gwamnati mai ci a halin yanzu, amma kuma sun koka da yadda ta takaita alawus-alawus na wata-wata a lokacin hutu.
Cletus Tse, wanda dalibi ne na shekarar karshe, a Jami’ar Joseph Sarwuan Tarka da ke Makurdi, ya bayyana yadda tsarin ya kyautata tare da taimaka wa harkar iliminsa.
“Da ba dan wannan rance da aka ba mu ba, da tuni na ajiye wannan karatu tun a shekarata ta biyu, amma wannan taimako na kudi; ya taimaka min wajen mayar da hankali kan wannan karatu nawa, ba tare da fargabar yadda za a iya nemo kudin d azan biya kudin makaranta ba.”
Amma duk da haka, Tse, ya nuna damuwarsa dangane da yadda ake gudanar da tsarin rabon kudaden.
“ Ya kamata gwamnati ta yi kokarin ganin ta gaggauta biyan alawus-alawus din, saboda da dama daga cikinmu na fuskantar tsaiko wajen biyanmu, wani lokacin har sai zangon karatu ya kusa karewa, wanda hakan ya saba wa tsarin shirin,” in ji shi.
Tse ya kuma yi kira da a kara karfafa manufofin samar da ayyukan yi, domin tabbatar da ganin cewa; wadanda suka ci wannan bashi, sun samu damar biya a kan lokaci.
“Abu ne mai kyau ganin cewa, bashin yana taimaka mana wajen ci gaba da karatu, amma kuma biyan bashin zai iya tabbata ne kadai, idan da zarar mun kammala karatunmu; ya kasance aiki yana nan yana tsumayinmu.
Ya kara da cewa, “Dole ne gwamati ta daidaita wannan shirin da samar da ayyukan yi, don gukun kada kuma ya zama wani nauyi ko wani abu daban.
Rashin Aikin Yi Ne Babban Dalilin Da Ke Sare Wa Dalibai Gwiwa – Prof Obiaraeri
A nasa bangaren, tsohon dan takarar Sanata, kuma Farfesa a fannin shari’a, Farfesa Nnamdi Obiaraeri, ya dora laifin a kan rashin amfani da kafafen yada labarai wajen sanar da daliban da kuma matsalar rashin aiki ga wadanda suka kammala karatunsu.
Tsohon shugaban tsangayar shari’a na jami’ar Jihar Imo ya bayyana cewa, “Dalilan da suka hana da dama daga cikin dalibai neman wannan tallafi sun hada da rashin bin hanyoyin da suka dace wajen sanar da jama’a daga hukumar ta NELFUND. Wasu kalilan daga cikin makarantu ne suka tsaya tsayin daka wajen fadakar da dalibansu dangane da bayar da wannan rance tare kuma da nusasshe irin fa’idar da ke tattare da shi, musamman ga wadanda suke da karamin karfi ko rashin galihu.
Ba Mu Da Masaniya A Kan Bayar Da Wannan Lamuni- Wasu Iyaye Daga Abiya
Wani abin mamaki shi ne, wasu masu fada a ji a matakai daban-daban a Jihar Abiya, ba su san da batun bayar da lamunin ba.
Har ila yau, sun dora laifin a kan wani bangare na hukuma kan rashin wayar da kan jama’a game da wannan lamari da kuma su kansu daliban, ya kamata a ce sun san da wannan shiri; fiye ma da iyayen nasu ko kuma masu kula da su.
Wani fitaccen mamba a kungiyar al’adun kabilar Ibo, Libinus Nzedike, shi ma ya ce; rashin sanin ya kamata ne ko kuma kwarin gwiwa ya jawo haka.
Ya kara da cewa, “Tazarar da ke tsakanin Kudu Maso Gabas da Arewa Maso Yamma da kuma Kudu Maso Yamma, abu ne day a kamata a tsaya a duba yadda ya kamata, domin gano musabbabin faruwar hakan,” in ji shi.
Wani babban sakatare a daya daga cikin ma’aikatun, kuma fira-ministan gargajiya na al’ummar yankinsa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya nuna rashin gamsuwa da yanayin matakin da yankin nasa ya dauka na rashin shiga shirin yadda ya kamata, su ma a dama da su.
Ya yi watsi da duk wani abin da aka ce, wanda ka iya haifar da wannan rashin shiga tsarin yadda ya kamata, domin ganin su ma an dama da su, yana mai cewa; hakan na iya faruwa sakamakon fargaba da juyayin tsawon lokacin da za a dauka na biya.
Wata shugabar mata a jam’iyyar APC (women leader), Nkechi Kanu, wadda ta yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, bisa kokarin bullo da wannan shiri na bayar da lamuni, ta ce; daliban na cutar da kansu kwarai da gasket a hanyar kin shiga a dama da su yadda ya kamata.
Har ila yau, a karshe ta yi kira ga hukumomin gwamnati da shugabannin siyasa, al’umma, addini da kuma na gargajiya; das u hada kai wajen wayar da kan jama’a game da wannan asusu ko lamuni na gwamnatin tarayya a kowane lungu da sako na fadin wannan kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp