Idris Aliyu Daudawa" />

Batun Hana Daukar Ciki Na Cikin Matsala A Duniya

Kamar dai yadda kafar bayanai dangane da yaan al’umma na duniya ta bayar da nata rahoton, daga majalisar dinkin duniya wasu kudade ko kuma taimako wanda ya shafi yawan jama’a na duniya (UNFPA) duk kuwa da yake ana samun yawan mata masu amfani da maganin hana daukar ciki na zamani, har yanzau mata suna fusknatar samun su magungunan.
Shi dai rahoton ya nuna irin karuwar da aka samu akan damar dasu mata suke da ita wadda ta shafi ala’amarin haihuwa wato daukar ciki, tun lokacin da ita UNFPA ta fara ayyukan ta shekaru hamsin da suka wuce (50). Sai dai kuma an samu wasu bayanai cewar milyoyin mata a kasashen duniya, har yanzu suna fuskanatar matsalolin tattalin arziki, jin dadai da kuma walwala, da kuma wasu sauran tarnakin da sukan hadu da su musamman ma idan abin ya zo kana bin da aya shafi lafiyar su.
A kasashen 51 wadanda ita UNFPA taba yi nazarin sub ta kuma nuna cewar kashe 57 ne mata wadandfa suke da aure ko kuma wadanda suke wata alaka sune suke da wata damar su ta daukar mataki,na ko za su iya saduwa da mijin su ko kuma ani abokin huldar tasu, amfani da maganin hana daukar ciki da kuma kula da lafiya.
A kasashen da suka ci gaba da kuma wadanda suke tasowa, samun ire-iren wadannan abubuwan da suka shafi shi al’amarin yana kasa sosai tsakanin mata matalauta, wanda kuma wannan yana shafar tattalin arzikin nasu.
Babban jami’in na UNFPA Natalia Kanem ya bayyana cewaa cikin bayanin shi, idan basu da ita damar, babau ta yadda za ayi su dauki wani mataki , akan abubuwan da suka shafi rayuwar su, wannan kuma ya kunshi lokacin da suke son su dauki ciki.

Exit mobile version