Fili na musamman domin makaranta, wanda zai rika ba wa kowa damar tofa albarkacin bakinsa kan abin da ya dame shi cikin zuciya, na rayywar yau da kullum, ko makamancin haka.
Filin namu na yau yana tafe da bayanin Abba Abubakar Yakubu, dangane da abin da ya dame shi cikin zuciya. Inda ya fara da cewa:
- Ra’ayoyinku A Kan Batun Hako Man Fetur A Yankin Bauchi Da Gombe
- Yadda Za A Kula Da Tafin Kafa Lokacin Hunturu
“Al’adun da kuke kyama, yanzu sun zama abin kwalliyar ku, saura ku karbi addininmu!”. Wadannan wasu kalamai ne na izgili da wani wanda ba musulmi ba ya rubuta a kasan jikin wani hoton wasu ma’aurata sabbin aure, wato Ango da Amarya, wanda aka dauka lokacin wani shagalin bikin aure.
Yanayin hoton ya nuna Angon cikin shigar kananan kaya ya sa kwat da wando da madaurin wuya, yayin da ita kuma Amaryar ta sanya farar rigar leshi da siffar dinkin Amaren turawa, kai ka ce dai bikin na wadanda ba musulmi ba ne.
Ba su kadai ba, hatta ga sauran abokai da kawayen Amarya ma duk irin wannan shiga ta kananan kaya suka yi, wasu ma kansu babu kallabi. Sai dai mai yiwuwa ka yi mamakin jin cewa, wannan Amarya da Ango ‘Ya’yan Musulmi ne, kuma ma cikakkun Hausawa ne, Amina da Bashir.
Ko da yake da gani ka san biki ne na wasu ‘ya’yan masu hannu da shuni, ‘yan siyasa ko wasu hamshakan ‘yan boko, saboda irin yadda aka kawata wajen bikin da kuma irin manyan mawakan da aka gayyata daga kudancin kasar nan.
Ba ina nufin yin irin wannan shigar ta sabawa koyarwar addini ba ne, wannan hakkin malamai ne su inganta ko su tsawatar a kai, amma ni abin da ya fi daukar hankalina shi ne; kayan da suka sa sun sabawa bikin aure na al’adar Bahaushe. Idan mun lura, saboda sabawar ce ma har wani yake ganin, saura kiris a ajiye addinin ma a gefe.
Na fara rubutu na da wannan salo ne domin nuna mana irin lalacewar da al’adun Malam Bahaushe suka samu kansu a ciki, musamman a bangaren bikin aure, kuma abin takaici masu fada a ji daga cikin al’ummar Arewa na daga wadanda ke kara angiza irin wannan lalacewar tarbiyya da al’ada.
Abin takaici ne yau ka je wajen bikin ‘ya’yan manyan kasar nan ka ga irin bidi’o’in da aka shirya da abubuwan da ake gudanarwa da sunan biki, wadanda ko kusa ba su yi kama da na Hausawa ba, kuma ma ba su dace da koyarwar addini ba.
Idan mai karatu ya lura da kalaman da na rubuta a farkon wannan sharhin na san zai yi tunanin lallai sauran abokan zaman mu su kansu suna mamakin yadda garin kwaikwayonsu da muke yi har mun kusa wuce makadi da rawa.
Kalaman da aka yi amfani da su a farkon wannan rubutu ba kirkira ba ne, tabbas! haka wani ya rubuta a shafin Instagram na wasu masu biki da suka sa hotunan auren su.
Ashe kenan idan har wadanda ba Hausawa ba za su rika mamakin yadda rayuwar mu ta canza, muka manta da namu kyawawan al’adun muka koma kwaikwayon wasu, za mu yi takaici da cizon yatsa kan wasu abubuwan da ke faruwa a rayuwar akasarin Hausawa ko ‘yan Arewa, ba kawai a sha’anin biki ba, har ma da sauran harkokin mu na rayuwa.
Matasa da iyayensu sun rungumi wasu halaye da suka saba da asalin tarbiyya, yakana, kunya da mutunta kai da aka san Hausawa da su.
Haka mutum zai yi ta ganin wasu abubuwan takaici da ke faruwa, tsakanin masu shirin aure, wanda ake kira hotunan kafin biki (Pre-Wedding Pictures), wani salon daukar hoto na ‘yan zamani.
Yadda za ka ga masoyan ko masu shirin auren na rungumar junansu, sumbatar juna da wasu sassan jikinsu, za ka rantse ma’aurata ne, sun yi aure tuni, ba wai shirin auren suke yi ba. To, in ma auren suka yi, haka addinin Musulunci da al’adar mu ta koyar a rika yi, don bayyana soyayya da burge mutane?.
Wasa a hankali muna kara yin baya baya da tarbiyyar mu ta addini da wanda iyaye da magabatan mu na kwarai suka dora mu a kai.
Muna rungumar wasu al’adu da ba su dace ba, kuma wata rana za mu ji kunyar a danganta mu da su, musamman idan yaran mu suka taso suka ga abubuwan da muka aikata a lokacin kuruciyar mu. Wanne abin koyi muke bar musu? Wacce rayuwa muke fatan su yi nan gaba, a matsayin su na manyan gobe?
Daga Abba Abubakar Yakubu.