A farkon sabuwar shekarar da muke ciki, ministan wajen kasar Sin ya sake kai ziyara nahiyar Afirka.
Jiya, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai ziyarar aiki a kasar Masar. Daga bisani, zai ziyarci kasashen Tunisia, da Togo, da Kodibwa. Hakan nan shekaru 34 a jere ke nan da ministan wajen kasar Sin ya fara kai ziyara nahiyar Afirka a farkon kowace shekara. Dangane da wannan batu, jaridar Al Akhbar ta kasar Masar ta rubuta wani sharhi cewa, hakan ya nuna “yadda kasar Sin take dora muhimmanci kan huldarta da kasashen Afirka, gami da kyakkyawar dangantakar dake tsakanin bangarorin 2, mai zurfi da daddaden tarihi.” Sai dai, bayan da abokan 2, wato Sin da Afirka, suka gana da juna a farkon sabuwar shekara, wadanne abubuwa za su tattauna a kai?
- Yadda Aikin Gine-gine Na Kasar Sin Suka Taimaka Wajen Gudanar Da Gasar Cin Kofin Afirka
- Ofishin Kula Da Harkokin Taiwan Na Majalisar Gudanarwa Da Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Sun Yi Tsokaci Kan Sakamakon Zabukan Taiwan
Da farko, za su tattauna batun zaman lafiya. A yayin da yake kasar Masar, ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Masar, da shugaban kasar, inda suka fi mai da hankali kan yanayin da ake ciki a zirin Gaza, gami da nuna buri da karfin hali, a fannin kare zaman lafiya da tabbatar da adalci. A wajen taron maneman labaru da ya gudana bayan ganawar, Wang Yi ya jaddada ra’ayin kasar Sin dangane da wannan batu, wato neman tsagaita bude wuta nan da nan, da ba da damar kai dauki ga masu bukata, da aiwatar da shirin kafa kasashe guda 2 a shiyyar don tabbatar da adalci ga Falasdinawa. Wannan ra’ayi na kasar Sin ya zama dai-dai da na kasar Masar, abin da ya sa kasashen 2 gabatar da wata hadaddiyar sanarwa a wannan karo.
Ban da haka, wani abin da ya kamata a lura da shi shi ne, a nata bangare, kasar Afirka ta Kudu ta kai kara gaban kotun kasa da kasa a kwanakin baya, inda take zargin kasar Isra’ila da aikata kisan kare dangi kan Falasdinawa a zirin Gaza, da bukatar kotun da ta umarci Isra’ila ta tsagaita bude wuta nan take. Bayan haka kuma, kasar Namibia ita ma ta nuna goyon baya kan matakin da Afirka ta Kudu ta dauka. Ta haka za mu fahimci cewa, kasashen Afirka da kasar Sin tare suke, a kokarin tabbatar da zaman lafiya da adalci a duniya.
Ban da bukatar samun zaman lafiya, an kuma mai da hankali kan maganar raya kasa da neman samun ci gaban tattalin arziki, yayin ziyarar Wang Yi a nahiyar Afirka a wannan karo. Kamar yadda jami’in ya gaya ma shugaba Abdel Fattah al Sisi na kasar Masar cewa, “Yayin da kasar Masar ke neman raya kanta, za ta iya dogaro kan daddadiyar huldar dake tsakaninta da kasar Sin.” Sai dai a hakika, Masar da sauran kasashen da Malam Wang Yi zai kai ziyara a wannan karo, tuni sun kasance abokan huldar kasar Sin, ta fuskar hadin gwiwa a fannin raya kasa. Misali, a kasar Masar, wani yankin hadin gwiwa na cinikayya, da bangarorin Sin da Masar suka kafa tare, ya riga ya janyo kamfanoni fiye da 140, wadanda suka bude rassansu a yankin, tare da samar da guraben aikin yi ga jama’ar kasar fiye da dubu 50. Kana a kasar Tunisia, kasar Sin ta ba da tallafin wani asibiti, da wani kwalejin horar da jami’an diplomasiyya, da wata cibiyar wasan motsa jiki ga kasar, kana kamfanonin kasar Sin na kokarin gina wasu manyan ayyukan more rayuwa a can, ciki har da wata babbar madatsar ruwa.
Sa’an nan a arewacin kasar Togo, wasu kwararru na kasar Sin masu fasahar aikin gona sun gudanar da gwaje-gwaje kan wani sabon nau’in shinkafa, wanda ya dace da yanayin lokacin rani, kuma ya samar da mafi yawan ’ya’ya fiye da nau’ika na baya. Yayin da a birnin Abidjan na kasar Kodivwa, wata sabuwar gadar da wani kamfanin Sin ya gina ta saukaka matsalar cunkuson ababen hawa. Bisa tushen wadannan abubuwan da suka shaida nagartacciyar huldar hadin kai tsakanin Sin da Afirka, ziyarar da Wang Yi ya kai nahiyar Afirka a wannan karo, za ta iya samar da karin nasarori.
Dalilin da ya sa ake samun kaunar juna tsakanin abokai, shi ne domin suna da tunani iri daya. Kana tunani na bai daya da kasar Sin da kasashen Afirka suke da shi, shi ne, yunkurin tabbatar da zaman lafiya da neman ci gaba. Yayin da ake ci gaba da fama da ra’ayi na babakere da nuna fin karfi, da yin mummunar takara ba tare da sanin ya kamata ba, gami da yin fito na fito, a sauran wurare daban daban na duniyarmu, kasar Sin da kasashen Afirka suna kokarin hadin gwiwa da juna, bisa burinsu da tunaninsu na bai daya, inda suke samar da gudunmow a kai a kai, don tabbatar da kyakkyawar makoma ga daukacin dan Adam. (Bello Wang)