Kusan za’ a iya cewa, ‘yan Nijeriya, za su fara samun sauki ganin yadda, matatar man fetur, ta garin Fatawal ta sake farfadowa domin gudanar da aiki.
Hakan ne ya sa dillalan man suka fara yin murna, musamman bayan da kamfanin mai na kasa NNPCL, ya sanar da cewa, an fara yin lodin man daga matatar.
- Dangote Ya Rage Wa ‘Yan Kasuwa Farashin Man Fetur
- Matatar Ɗangote Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasar Kamaru
Sai dai, wannan murnar ta dillan man ta sa sun fara yin tunani kan yadda farashin man zai kasance, hakanan su ma ‘yan Nijeriya, ne a cikin irin wannan fargabar ta farashin man.
La’akari da yadda gwamnatocin baya suka kasa sake farfado da matatar, amma a yanzu gwamnatin mai ci, ana ganin ta samu nasara kan sake farfado da matatar.
Kazalika ma, me yiyuwa gwamnatin ta bayar da umarnin a gyara matatun man na Warri da kuma Kaduna.
Bisa martanin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mayar na dawo da aikin matatar man ta Fatawal, an kuma ruwaito cewa, Tinubu ya umarci NNPCL da ya fara aiki a cikin gaggawa na sake farfado da matatar man ta Fatakwal da kuma sauran matatun biyu.
‘Yan Nijeriya dai, na ci gaba da jira, domin ganin cewar, ko abin da zai auku, zai kasance wani sauki ne, ga matsalar da fannin samar da makamashin kasar ke fuskanta.
Bisa ga dukkan alamu, kafa mamatar mai ta Dangote da kuma farfado da ta Fatakwal, za su share wa ‘yan Nijeriya hawayen, kalubalen da suke fuskanta na karancin samar da man da kuma dakile shigo da man daga ketare.
Shekaru da dama da suka gabata, matatun na Fatakwal, Warri da kuma Kaduna, gwamnatocin baya sun zuba biliyoyin dalali domin sake farfado da su, sai dai, kuma kash! babu wani aikin azo a ganin da aka gudanar.
Bisa wannan ci gaban da aka samu ne, na sake farfado da matatar ta Fatakwal, hakan zai sa a kara samar da man da sauran dangoginsa a Nijeriya, musamman farashinsa.
Sai dai kuma, masu fafutukar a fannin mai da iskar Gas a kasar, da ke son ganin an sake gyaran matatun man kasar, sun kasance suna ja da baya duba, wajen yabawa kan sake farfado da matatar ta Fatakwal.
Sai dai kuma, a ra’ayinsu, idan aka ci gaba da kokarin samar da man a kasar, hakan zai sa a samar da wadatacen sa da kuma sa gasa kan ragin farashin sa.
Amma bisa ra’ayin wannan jaridar, shi ci gaban da aka samu meyiyuwa ne daga karshe, ba zai kai na dogon zango ba, domin fargabar mu ita ce, ‘yan hana ruwa gudu a fannin, suna iya hanasu yin wani katabus wanda hakan zai dakushe kyakkyawar niyyar da gwamnatin mai ci take da shi, na samar da wadataccen man a kasar
Hakanan ma, wadannan ‘yan hana ruwan gudun na da matukar karfi da dukiyar da za su iya yin amfani da ita domin su hana su yin abinda ya kamata sanayyarsu, wajen hana abinda ya kamata, na ci gaban da ka samu.
Akasarin ‘yan Nijeriya na sane da cewa, jigajigan ‘yan Nijeriya da ke a fannin man, sun fi mayar da hankali ne ga kasuwar mai ta kasar nan.
A saboda haka, mun sa ido domin mu ga idan har za a iya tuge bututun man Zumar da ke a bakinsu, wanda ya shafe shekaru, yana manne, a bakinsu.
Muna goyon bayan wannan kokarin na sake farfado da matatar ta Fatakwal, matukar dai idan hakan zai samarwa ‘yan Nijeriya saukin samun man, musamman ma idan an yi la’akari da matsalar da cire tallafin mai, ta haifar a kasar.
Sai dai kuma, har yanzu bamu da wani yakinin cewar, sake farfado da matatar man ta Fatakwal, zata samarwa ‘yan Nijeriya wani sauyi.
Amma duk da haka, muna fatan sauyin zai tabbata, musamman ma yadda a shekarun baya, aka rinka karya lagon fatan ta ‘yan Nijeriya da kuma barinsu a cikin magagin samun sauki.
Akasarin kayan da ake amfani da su wajen sake farfado da matar man, an sayo su ne, da kudin kasar waje, duk da cewa, mun san irin darajar da kudin kasar ya ke da shi a kasuwar cikin gida da hukuma ta san da ita, da kuma a kasuwar bayan fage.
Bugu da kari, za a dora farashin fanfon man ne, daidai da na farashin danyen mai a kasuwar duniya, wanda daukacin yin hakan ne, zai kare a kan masu sayen man, saboda kuwa , ba su da wani zabi cewa, illa dole ne, sai su sayi man.
Ko yaya dai abin ya yake, muna fatar ci gaban da aka samu zai taimaka wajen inganta samar da mai a wannan kasar tamu.
Babu wani abinda zai karya mana kwarin gwiwa bisa jajicewarmu mu na cewa, farashin man, zai karye warwas, musamman ma saboda da ‘yan Nijeriya su samu saukin sayen man a cikin farashi mai rahusa.
Daga karshe annan jaridar, za ta yi matukar murna ta tabbatar da abinda take da yakini na kara samar da wadataccen man fetur a wannan kasar.