Biyo bayan sauke Birgediya-Janar Muhammad Kaku Fadah dava mukaminsa na darakta-janar na Hukumar Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC), daraktar sashen Kimiyya da Fasaha, Christy Uba, za ta rike mukamin na wucin gadi.
A makon da ya wuce ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya cire Fadah daga kan mukamin.
- Masari Ya Barke Da Kuka Yayin Gabatar Da Kasafin Kudinsa Na Karshe
- An Yi Ganawa Tsakanin Ministocin Tsaron Kasashen Sin Da Amurka
Buhari a ranar 17 ga watan Nuwambar 2022 ne, ya amince da a cire Fadah daga kan mukamin.
Rahotannin sun ce, shugaban ya bayar da umarnin a cire Fadah ne, saboda gazawarsa na iya tafiyar da hukumar.
A cikin wata sanarwar da kakakin hukumar ya fitar, ta ce ganin cewa, Christy ita ce babba yanzu a hukumar shi ya sa shugaban kasa ya amince da ta rike mukakin na wucin gadi kafin a nada wani sabon shugaban.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp