Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta amince da gina sabon filin wasa mai iya ɗaukar mutane 100,000.
Ana sa ran za a kammala aikin cikin shekaru biyar masu zuwa.
- Zafin Rana Zai Tsananta A Wasu Jihohin Nijeriya – NiMet
- Nijeriya Ta Shigo Da Man Fetur Na Naira Tiriliyan 12 A 2024 – Rahoto
Ɗaya daga cikin mamallakan ƙungiyar, Sir Jim Ratcliffe, ya ce burinsa shi ne gina filin wasa mafi ƙayatarwa a duniya, wanda zai zama sabon filin wasa na Manchester United bayan shafe shekaru 115 tana amfani da Old Trafford.
Ana hasashen cewa sabon filin zai lakume kimanin dala biliyan 2.5.
A halin yanzu, Manchester United na fuskantar ƙalubale a gasar Firimiya, inda take matsayi na 14 bayan buga wasanni 28.
Duk da haka, kungiyar za ta ci gaba da amfani da Old Trafford har sai an kammala sabon filin wasan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp