CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Bayanan Da Aka Fitar A Taron Da Aka Yi A Wuhan Sun Bata Ran “Masu Ra’ayin Makirci”

by CRI Hausa
February 10, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Bayanan Da Aka Fitar A Taron Da Aka Yi A Wuhan Sun Bata Ran “Masu Ra’ayin Makirci”
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A ranar 9 ga wata, a yayin taron manema labaru da hadin gwiwar tawagar kwararru ta kasar Sin da WHO kan nazarin asalin kwayar cutar annobar COVID-19 ta gudanar a birnin Wuhan na kasar Sin, shugaban tawagar a bangaren ketare Peter Ben Embarek ya bayyana cewa, maganar da aka yi wai cutar ta bulla ne daga dakin gwaje-gwaje, hakan “ba zai yiwu ba”, don haka, ba za a ci gaba da binciken asalin ta wannan hanya ba. Wannan sakamakon da aka samu ya kara wanke sunan cibiyar nazarin cututtuka ta Wuhan, wanda aka dade ana bata sunanta. A nasu bangaren, wadancan ‘yan siyasa da kafofin watsa labarai na Amurka da na yammacin duniya da suka kirkiri wadannan makircin, ba za su ji dadi ba.
Ban da wannan kuma, game da bakin fenti da aka shafawa kasar Sin cewa, wai ta kawo cikas ga binciken da ake kan asalin cutar. A cikin kwanaki fiye da goma da suka wuce, mambobin tawagar kwararru na WTO da kasar Sin, sun yi nazari kan muhimman bayanai game da yaduwar annobar, sun kuma gudanar da bincike a hukumomi guda 9, ciki har da asibitin Jinyintan, kasuwar sayar da kayan teku ta Huanan, da cibiyar nazarin cututtuka ta Wuhan da dai sauransu, inda suka kuma tattauna da ma’aikatan lafiya, ma’aikatan cibiyar nazarin, masu aikin nazarin fasaha, jami’ai da ‘yan kasuwa, ma’aikatan al’umma, wadanda suka warke daga cutar, iyalan ma’aikatan lafiya da suka rasu sakamakon cutar, da kuma mazauna wurin da makamantansu.
Kamar yadda mamban tawagar a bangaren WHO Dr. Peter Daszak ya fada a yayin da yake zantawa da kafar yada labarai ta Bloomberg, “Mun ba da shawara kan inda za mu ziyarta, da kuma wadanda za mu tattauna da su. Mun yi bincike a duk wuraren da muka gabatar, mambobin tawagar a bangaren kasar Sin suna son kai mu wuraren sosai.”
Ana iya ganin cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana gudanar da komai a bayyane game da binciken gano asalin cutar a duk duniya, kuma tana nuna goyon baya ga WHO wajen gudanar da ayyukan da suka dace, wanda ke nuna yadda babbar kasa dake sauke nauyin dake kanta. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

SendShareTweetShare
Previous Post

Wasan Nuna Wake-wake Da Raye-raye Na Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Huldar Diplomasiyya A Tsakanin Sin Da Najeriya

Next Post

NIS Ta Yaye Mataimakan Kwanturola Janar Da Suka Halarci Kwas Na 10

RelatedPosts

Greenwood Zai Iya Zama Kamar Ronaldo Ko Messi, Cewar Solkjaer

Greenwood Zai Iya Zama Kamar Ronaldo Ko Messi, Cewar Solkjaer

by CRI Hausa
19 mins ago
0

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunner Solkjaer,...

Zamu Mu Iya Sake Lashe Kofin Zakarun Turai Bana – Lewandowski

Zamu Mu Iya Sake Lashe Kofin Zakarun Turai Bana – Lewandowski

by CRI Hausa
20 mins ago
0

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen,...

Na Fara Tunanin Ta Yadda Za Mu Doke PSG – Koeman

Na Fara Tunanin Ta Yadda Za Mu Doke PSG – Koeman

by CRI Hausa
24 mins ago
0

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bayern...

Next Post
NIS Ta Yaye Mataimakan Kwanturola Janar Da Suka Halarci Kwas Na 10

NIS Ta Yaye Mataimakan Kwanturola Janar Da Suka Halarci Kwas Na 10

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version