Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya ziyarci Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, inda ya ziyarar wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
Obi, wanda ya shiga cikin jihar a cikin wani jirgin saukar ungulu, ya ce abin da ya gani abun tausayi ne kuma babu wata jiha da za ta iya jurewa irin wannan barnar.
- Juncao, Ciyawar Da Ke Rungumar Makomar Dan Adam Ta Bai Daya
- Gwamnatin Jigawa Ta Hada Gwiwa Da Kasar Netherland Don Kawo Karshen Ambaliyar Ruwa
Don haka ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da a gaggauta ayyana dokar ta-baci a kan lamarin ambaliyar a Bayelsa.
Obi ya ce, “Na ga illar ambaliya, na je wasu wurare, kuma ban taba ganin irin wannan barnar ba, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta-baci a Jihar Bayelsa.
“Babu wata jiha da za ta iya tinkarar irin wannan bala’i da kanta, ina kuma kira ga kasashen duniya da kungiyoyin bayar da agaji da su tallafa wa jihohin da abin ya shafa, a Bayelsa muna bukatar taimako, wannan barnar ba za a iya misalta ta ba.”
Obi ya ce ya je Yenagoa ne domin jajanta wa gwamnatin jihar da wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.
Gwamna Douye Diri wanda ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a gidan gwamnati da ke Yenagoa kafin ya zarce zuwa sansanin ‘yan gudun hijira da ke tafkin Ox-Bow domin ganewa idanunsa wadanda lamarin ya shafa, ya gode wa Obi bisa nuna goyon baya da ya yi, ya kuma bukaci sauran kungiyoyi da daidaikun jama’a masu kishin kasa da su hada kai da Gwamnatin Jihar wajen bada tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.
LEADERSHIP ta rawaito cewar ziyarar da Obi ya kai Bayelsa na zuwa ne kwanaki kadan bayan irin wannan ziyara da ya kai ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Benuwe.
Tun da farko dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP ya sanar da dakatar da yakin neman zabensa saboda iftila’in ambaliyar ruwa wasu sassan kasar.