A ranar Asabar ce Bayern Munich ta sha kashi a hannun Eintracht Frankfurt da ci 5-1 a gasar Bundesliga ta bana abin da ya sanya alamar tambaya akan makomar kocin kungiyar Thomas Tuchel.
Lokacin da Niko Kobac ya ga kungiyarsa ta Bayern ta yi rashin nasara da ci 5-1 a hannun Frankfurt a watan Nuwambar shekarar 2019, an kore shi cikin awanni 24.
- Jami’ar Ambrose Alli Ta Lashe Lambar Yabon Fasaha Ta Nijeriya
- Akwai Yiwuwar Gwamnati Ta Kara Yawan Kasafin Kudin 2024 – Ministan Kudi
A wancan lokacin Bayern Munich suna matsayi na hudu akan teburin Bundesliga, daidai da inda Thomas Tuchel ya sami tawagarsa a yanzu.
An fara nuna shakku akan Tuchel tun a farkon kakar wasa ta bana lokacin da aka doke Bayern da ci 3-0 a cikin filin wasansu a Supercup da RB Leipzig.
A farkon watan da ya gabata, kungiyar Saarbrucken wadda take mataki na uku ta fitar da su daga gasar cin kofin gida.
Harry Kane ya yi fice a gaba, wanda ya fi zura kwallaye a gasar Bundesliga, sai dai kwallayen da ya jefa a raga bai sa Bayern Munich ta ci gaba da jan ragamar gasar ta Bundesliga ba.
Bayern ce ke kan gaba wajen zura kwallaye a gasar Bundesliga, daga ciki akwai nasarar da ta samu akan Borussia Dortmund da ci 4-0, amma har yanzu ba ta samu galaba a kan sauran kungiyoyin da ke matsayi na huddu a teburi ba.
Daraktan wasanni na Bayern Christoph Freund ya ba da shawarar cewa matsala ce ta yanayi domin kuwa duk kungiyar ta yi muni.
Tsohon dan wasan tsakiya na Bayern Stefan Effenberg ya dora laifin akan ‘yan wasan tsakiyar kungiyar Joshua Kimmich da Leon Goretzka.