Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich na duba yiwuwar daukar dan wasan gaban na Manchester United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, bayan ta yi amanna da hazakar da ya nuna a zaman aron da ya yi a Aston Billa a kakar da ta gabata.
Dan wasan dai yana cikin ‘yan wasan da kungiyarsa ta Manchester United ta saka a kasuwa idan har an samu masu saya.
- Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali
- Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau
A watan Janairun wannan shekarar ne Rashford yayi zaman aro na watanni shida a kungiyar Aston Billa sakamakon Rashin jituwa da suka samu da kociyan Manchester United din, Ruben Amorim, wanda sakamakon hakan ya daina amfani da shi a wasa kuma daga karshe ma kungiyar ta saka shi a kasuwa.
A cikin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Manchester United da Aston Billa, idan har Rashford yayi kokari za ta siye shi a kan kudi fam miliyan 40, amma daga baya, bayan an kammala wasa ta kare Aston Billa ta ce ba za ta iya saya ba.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa dan wasan ne da kansa ya ce baya son komawa Aston Billa saboda ba za su buga kofin zakaru na Champions league ba a kakar wasa mai zuwa, wanda hakan ya sa dan wasan aka bayyana cewa zai koma Manchester United har sai an samu kungiyar da za ta iya sayansa.
Rashford dai ya fi son komawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona domin yana ganin zai iya buga abin a zo a gani a kakar wasa mai zuwa sai dai ita kuma Barcelona ta fi son dan wasa Nico Williams na kungiyar Athletico Bilbao ta kasar Spaniya, wanda shima yake son komawa Bardelona da buga wasa idan har Barcelonan za ta iya biyan kudin da aka yi masa farashi.
Kungiya ta kwana-kwanan nan da ta nemi Rashford ita ce kungiyar Bayern Munchen ta Jamus, bayan da Liberpool ta ce ba za ta sayar mata da Luiz Diaz ba, ana ganin yanzu kungiyar za ta karkata akalarta zuwa neman Rashford. Kungiyoyi irinsu Newcastle United da Tottenham da kungiyoyi daga Saudiyya duka sun nuna sha’awarsu ta sayan dan wasa Rashford.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp