Noman Kwakwamba na daya daga cikin fannin aikin noma da ke kara habaka a kasar nan, inda kuma kara nomanta, zai kara bunkasa tattalin arzikin kasar, samar da ayyukan yi da kuma kara samar da kudaden shiga manimanta.
Har ila yau, yawan bukatar da ake da ita, na kara karuwa a kasar nan, ana kuma samun samfari-samfarin ta, haka kuma bukatar da ake da ita, ya nuna cewa na kara karu wa a kasar nan, inda kuma akasarin mutane su na yin amfani da ita domin kara lura da lafiyarsu fiye da sauran kayan lambu.
Shekaru da dama da suka shige, shugaba a kamfanin aikin noma na Beggie Concept Ayo Akinfolarin ya aiwatar da yadda ake nomanta, inda kuma hakan ya kara samar ma sa da kudaden shiga masu ya wa.
Ayo Akinfolarin ya bayyana cewa, bukatar ta Kwakwamba a kasar nan na karu wa, inda ya kara da cewa, ana yin amfani da ita a cikin abinci da ban da ban.
Ya sanar da cewa, ya samu dimbin riba ta hanyar noman Kwakwamba, inda ya ci gaba da cewa, ta hanyar nomanta, ya kuma samar da Iri mai ya wa wanda har ya na tura su zuwa wasu wurare.
A cewarsa, ana samun dimbin riba a nomanta, inda ya yi nuni da cewa, wasu na yi wa sana’ar noman Kwakwamba a matsayin injin ATM saboda yadda ake samun kudi a cikin nomanta a cikin dan lokaci.
Sai dai Ayo Akinfolarin ya kuma yi nuni da cewa, akan fuskanci yin asara a yayin nomanta, in har manomi bai yi kyakyawan tsarin nomanta ba, inda ya kara da cewa, daga shuka Irinta 300 a cikin sauki za a iya girbin day a kai kilomita kimanin 7,500 a karshen kakar nomanta.
Ayo Akinfolarin ya bayyana cewa, buhun Kwakwamba mai nauyin kilo giram 35, ana sayar da shi daga naira 3,500 zuwa naira 7,000.
A cewar Ayo Akinfolarin, kadada daya ana samun daga buhu 800 zuwa buhu 1,300, inda za a iya samun kudin shiga har naira miliyan 5, inda ya kuma bai wa sababbin shiga nomanta shawara kan su tabbatar da sun a yin nomanta ta hanyar kimiyya, musamman a lokacin yin noman rani.
Ayo Akinfolarin ya kara da cewa, Kwakwambar da aka noma a fili ta na kai wa daga kwanuka 70 zuwa kwanuka 110 kafin ta nuna, amma wacce aka noma a kebabbaen wuri, ta na kai wa tsawon watannin shida kafin ta nuna in har an ba ta kulawar da ta kamata.
Ya bayar da shwara a rika gudanar da yin kasafi, tanadar isassun kudade da kuma kayan aiki kafin a fara yin nomanta, inda ya yi nuni da cewa, ga wanda sabon shiga cikin fannin ne, zai iya yin aron kadada daya daga kan naira 25,000, sai kuma takin zamani na naira 200,000, takin gargajiya kuma kan naira 50,000, maganin kwari kan naira 70,000, da ingantaccen Iri kan naira 240,000, sai kuma kudin kwadago kan naira 240,000 da suransu.
A daukacin fadin duniya, Irin kukumba a kasuwa ya na kai wa kan dala miliyan 1,939.6 a shekarar 2027.