Tsohon dan wasan gaban Manchester United, Wayne Rooney ya samu sabon aikin horarwa bayan barin D C United a satin da ya gabata.
Birmingham City ta sanar da nadin Wayne Rooney a matsayin sabon kocin kungiyar.
- Mutane 156 Sun Kamu Da Cutar Diphtheria, 20 Sun Mutu A Kaduna
- Charles Onunaiju: Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Sanya Sabon Ci Gaba A Nijeriya
Shahararren dan wasan na Ingila da Manchester United, Rooney ya maye gurbin John Eustace a St Andrews bayan ya bar DC United ta kasar Amurka a makon jiya.
Rooney, wanda ya kasance kocin Derby County tsakanin Nuwamba 2020 zuwa Yuni 2022, zai kasance tare da tsoffin abokan wasansa Ashley Cole da John O’Shea a matsayin wani bangare na mataimakansa.