Wasu ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hare-hare a wasu sansanonin soji a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji da dama tare da jikkata wasu.
Hare-haren sun faru ne a sansanin soji da ke Wajirko a Damboa da kuma sansanin Wulgo a Gamboru Ngala da yammacin ranar Litinin.
- Majalisa Ta Yi Watsi Da Kara Akan Akpabio Kan Zargin Neman Yin Lalata Da Natasha
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [18]
Rahotanni sun nuna cewa an kashe wasu daga cikin mayaƙan Boko Haram a lokacin musayar wuta.
Haka kuma, an ce wani Kwamandan soji da ya je kai ɗauki ya taka nakiya, wadda ta fashe, lamarin da ya ƙara jikkata wasu sojoji da ma rasa rayukan wasu.
Sansanin sojin Wulgo yana kusa da iyakar Najeriya da Kamaru, inda sojojin ƙasashen biyu ke haɗin gwiwa wajen yaƙi da ‘yan ta’adda.
Ko da yake an samu rage yawan hare-haren Boko Haram a baya-bayan nan, rahotanni na nuna cewa suna ƙara kai hare-hare kwanan nan.
Tun daga shekarar 2009, rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 200,000 tare da tilasta wa miliyoyin mutane tserewa daga gidajensu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp