Daga Muazu Hardawa, Bauchi
A jiya ne aka buɗe taron ƙungiyar matan gwamnonin Arewa a wurin shaƙatawa na Yankari da ke Jihar Bauchi. Taron Wanda ya samu halartar matan gwamnonin da muƙarrabansu, ya tattauna kan batutuwa da dama game da irin ƙalubalen da Mata ke fuskanta a arewacin Nijeriya.
Uwargidan gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar cikin jawabinta na buɗe taron ta yaba da ƙoƙarin uwargidan shugaban kasa Hajiya Aisha buhari game da shirinta na inganta rayuwar matan Nijeriya don haka ta CE an shirya wannan taron ne domin duba yadda za inganta rayuwar mata a gidajensu ta hanyar Samar musu da Sana’a da kuma Bunkasa karatun yara mata. Don haka ta bukaci mazajensu kan su temaka musu wajen cimma wannan buri nasu.
Haka kuma ta roki mata a Nijeriya da su himmatu wajen Neman abin kan su don rayuwarsu ta inganta. Ta kara da cewa a jihar Bauchi sun fito da manufofi masu yawa na temakon mata don inganta musu rayuwa.
Har wa Yau ya kara da city wa gwamnonin arewan za su taimaki matana masu wajen inganta rayuwa mata a jihohin da Duke mulki duk da irin matsalolin da ake ciki a Arewa fatar su shi ne a kawo karshen kuncin da mata ke ciki a wannan lokacin.