A taron shekara-shekara na kamfanin Siminti na BUA karo na 8, Shugaban Kamfanin, AbdulSamad Rabiu, ya bayyana cewa, shirin kamfanin na sayar da siminti kan Naira 3,500 a kan kowane buhu ya ci tura.
Ya ce dole ce ta sa suka mayar da farashin Naira 7,000 zuwa Naira 8,000 kan kowane buhu.
- Jihohi 21 Na Neman Bashin Naira Tiriliyan 1.65 Duk Da Ƙarin Kuɗaɗen Shiga
- Abin Da Ya Sa Muka Yi Zanga-Zanga A Kaduna -Masu Sharar Titi
Rabiu, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda dillalai suke dakile shirin kamfanin na samar da siminti mai sauki ga masu amfani da shi.
Duk da wannan cikas, Rabi’u ya jaddada cewa simintin BUA ya yi ta kokarin daidaita farashin, inda ya ce farashin simintin a halin yanzu ya yi kasa fiye da yadda yake.
Ya bayyana irin tasirin da farashin makamashi ke haifarwa, musamman tashin farashin iskar gas, wanda ya karawa kamfanin kudaden da ake kashewa wajen gudanar da aiki.
Rahoton kudi da aka gabatar a wajen taron ya nuna cewa kamfanin simintin na BUA ya samu karuwar kudaden shiga da kashi 27.4%, inda ya kai Naira biliyan 460 a shekarar 2023.