Connect with us

WASANNI

Buffon Zai Dawo Buga Wa Kasar Italiya Wasa

Published

on

Shahararren mai tsaron gida da ke kungiyar PSG, Gianlugi Buffon, ya ce a shirye ya ke, ya janye ritayar da ya yi daga buga wasanni a matakin kasa, domin ya koma bugawa kasarsa ta Italiya wasa.
A baya Buffon ya sanar da yin ritaya daga bugawa Italiya wasa ne bayan da suka gaza samun tikitin halartar gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar Rasha wanda kasar Faransa ta lashe.
Rashin nasarar da Italiya ta yi a hannun kasar Sweden ne, ya hanata damar zuwa Rasha, wanda kuma karo na farko kenan da Italiya ta gaza samun nasarar halartar gasar cin kofin duniya cikin shekaru 60.
Shi ma a nashi bangaren, mai horar da tawagar Italiya, Roberto Mancini, tsohon kociyan Manchester City ya ce yana fatan Buffon din zai dawo domin cigaba dawakiltar kasar a wasannin da kasar zata fara na neman zuwa gasar cin kofin nahiyar turai.
Buffon dai ya lashe kofin duniya da kasar Italiya a shekara ta 2006 da aka buga a kasar Jamus bayan sun doke kasar Faransa a wasan karshe a bugun fanareti kuma shine kofi na hudu da kasar Italiya ta lashea tarihin kofin duniya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: