Bugawar zuciya a lokacin da dan wasa yake tsaka da wasa dai ba sabon abu bane ga ‘yan wasa da likitoci da su kansu masu kallon kwallon kafa kuma a ko ina a fadin duniya.
Damar Hamlin, shahararren dan wasan kwallon kafar Amurka ne, shi ne dan wasa na baya-bayan nan da ya gamu da matsalar bugun zuciya yayin buga wasan kwallon kafa.
Dan wasan mai shekara 24 a duniya ya fadi kasa lokacin da ake buga wasa bayan da suka yi karo da wani dan wasa mintoci kadan a tashi wasa kuma likitoci sun tabbatar da cewa ya gamu da bugun zuciya – wanda hakan ke nufin zuciyarsa ta daina bugawa yadda ya kamata na samar wa wasu sassan jikin jini sannan likitocin sun yi kokari wajen ganin sun ceto rayuwarsa a cikin filin kuma yanzu haka yana kwance cikin mawuyacin hali a asibiti.
Amma likitocin da suke jinyarsa ba su bayyana tatamaimen matsalar da take damunsa ba sai dai wani abu da ke janyo bugawar zuciya shi ne kaduwa wanda ake kira da commotio cordis.
A wannan yanayi, idan wani abu ya bugi kirji, hakan zai iya janyo bugawar zuciya, inda zuciya ba za ta yi aiki yadda ya kamata ba sannan wannan wani na’u’in bugun zuciya ne na daban wanda ke faruwa idan jijiyoyi suka daina samar da jini wanda hakan kan janyo matsala ga zuciya saboda nauyin bugu.
Ba’a dai san irin raunuka da Hamlin ya samu ba a cikin zuciyarsa daga karon da ya yi da wani dan wasa sannan ko zuciyar sa ta samu matsala amma wata matsala ta zuciya da ‘yan wasa ke fuskanta shi ne cuta ta zuciya da ke shafar jijiyoyi.
Mutane da ke da irin wannan matsala za a iya ganinsu cikin koshin lafiya ba tare da wasu alamu da ke nuna cewa suna fama da wata lalura ba sai dai yanayi ne da ke sanya jijiyoyin zuciya kara girma, inda hakan ke sakawa da wuya jini ya kai zuwa zuciya, wanda hakan ke nuna akwai wata matsala a kasa.
Masu gwagwarmayar adawa da rigakafi a kafofin sada zumunta sun dora laifin matsalar bugun zuciyar Hamlin kan alluran cutar korona duk da cewa ba su bayar da wata hujja ba.
Sun kuma tattara alkaluman ‘yan wasan da suka mutu domin karfafa hujjarsu sai dai, a cewar wani bincike da aka yi a shekarar 2016, akwai akalla mutane 100 zuwa 150 da ke mutuwa a Amurka sakamakon bugun zuciya a kowace shekara ya yin buga wasanni.
A watan Maris din shekarar 2022, hukumar shirya gasar kwallon kafa ta Amurka, ta ce an yi wa kashi 95 na ‘yan wasan rigakafin cutar korona kuma Hamlin dai ba shi ne dan wasa na farko ba da ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da wasa.
Domin shi ma dan wasan kasar Denmark, Christain Eriksen, ya gamu da bugun zuciya a shekarar 2020 da ta gabata yayin buga wasa a gasar Euro 2020, inda ya kusa rasa ransa.
Likitoci sun yi amfani da wata na’ura domin farfado da zuciyarsa, inda ta dawo aiki yadda ya kamata kuma tun daga wancan lokaci aka samar da wata karamar na’ura mai suna ICD domin ci gaba da duba zuciyarsa.
Eriksen ya ce babu ko da wani a cikin iyalansa da ya taba gamuwa da matsalar bugun zuciya, saboda ana yi masa gwaji iya rayuwarsa ta kwallo kamar sauran manyan ‘yan wasa.
A shekarar 2012, wani dan wasa mai suna Fabrice Muamba, ya yanke jiki ya fadi a cikin fili a lokacin da zuciyarsa ta daina aiki sannan an samar da na’urori 15 domin farfado da zuciyarsa.
Idan aka bai wa mutum agajin lafiya ta gaggawa ya kan samu sauki amma ba ko yaushe ake samun nasarar ceto rayuwar mutum ba kuma a cewar binciken gidauniyar Cardiac Risk in the Young, mutum 12 ‘yan kasa da shekara 35 ke mutuwa a Birtaniya a kowane mako sakamakon bugun zuciya.