Buhari Ne Shugaban Da Ya Fi Kowanne Aiki Da Dimokradiyya –Dr. Bature Abdul’azeez

Ya kamata ‘yan Nijeriya su sake zabar Buhari, saboda a yau shi ne mai amanar da zai tsare NNPC daga sayarwa, mutanen da suka ce za su sayar da NNPC abaya fa su suka sayar da NEPA, ba a ga kudin ba, suka sayar da NITEL ba a ga kudin ba, kai a kwai lokacin da Obasanjo ya kadawa jiragen Nigeria Airways guda tara gwanjo gabaki dayansu, ban da jiragen da sayar lokacin da ya fara mulkun nan. Kuma tsakanin jirigi mai rai da matacce Nijeiya tana da ya fi guda 40, amma duka shi ya sayar da su, kuma da ya sayar da su ina ya sa kudin, me aka yi da kudin? To haka ma idan aka sayar da NNPC, bayan an sayar da ita za a samu cikin ukuba cikin bala’i, sannan kudin a rasa inda suka yi. Saboda haka wadancan kayayyaki da aka sayar na Nijeriya suna da yawa, akwai kayayyakin da wallahi tun lokacin mulkin mallaka yake, a takaice ka yi ta sayar da su daya bayan daya, kuma su ma su sayarwar su ne suka rika sayar da junansu da ‘yan’uwansu. Abubuwan da aka sayar kadarorin Nijeriya ne wadanda suke a yanzu kafin a mayar da wadancan kadarori sai an da gaske. Amma duk da sun sayar da su ina kudin suke? Sun rabe, kuma da dama kayayykin da suka sayar kawunansu suka sayarwa.
Muna rokon Shugaba Muhammadu Buhari idan Allah ya sa ya dawo gwamnati, a yi binciken kadarorin nan lallai za a samu wadanda suka saye su, saboda a Gwamnatin Obasanjo idan har an yi bincuke lallai ba za su ka labari ba. saboda haka ‘yan Nijeriya su fahimci cewa Buhari shi ne, rufin asirin Nijeriya, kuma Buhari shi yake da gaske wajen gina Nijeriya, kuma Buhari shi yake daidai da talakan Nijeriya, don har yanzu shi ma ba don mulki ba za ka iya kiransa talaka.
Ai ka ga lokacin da yah au mulki sai ya bayyana kadararsa aka rubuta kamar yadda dokar kasa ta tanada, kuma ka saurara ka ga lokacin da zai sauka abin da ya mallaka ba zai ninka sau goma ba, to ko da ya ninka sau goma a da fa abin da mallaka bai fi miliyan 100 ba in ma ya kai, to idan ya ninka sau goma ai biliyan daya ma kenan, to wallahi idan Buhari ya sauka ba za aka samu biliyan daya a wurinsa ba.
Amma mutanen nan da kullum suke zugugu, suka nemi wani dan takara suka sa shi a gaba, suna kokarin su dakushe yunkurin Buhari kar ya kai labari, wallahi Allah na rantse suna da arzikin da ya fi na Gwamnatin Nijeriya, muna da dala biliyan 40 ko in ce da biyar. To wadannan a cikinsu akwai wanda yake da dala ta fi biliyan 20, in masu son talakawa ne su fito su raba wa talakawan mana, ko su taimake su da abin da ya kamata su taimake su, ka ga kenan su suka yi wa kasar karkaf.
Amma duk kokarin da Buhari yake yi su a ganinsu su mai da masa da hannun agogo baya, suna ganin idan Buhari ya sake dawowa mulki, to fa kashinsu ya bushe. Kai dan Nijeriya, Buhari ne rufin asirin Nijeriya, kuma Buharine rufin asirinmu. Wadannan mutane lokacin da suka hau za ka ji mutanen da ba su san tarihin komai ba suna cewa Arewa ba a aiki, Arewa ba a yi mata komai ba, wallahi ba ku san komai ba, ayyukan da Buhari ya shirya wa Arewa a yanzu a dannan lokacin da kuke gani sai dai mu yi addu’ar Allah ya sa a gama lafiya.
Su wadancan fa ba su da burin da wuce su azurta kansu da ‘ya’yansu, kuma tsari ne wanda sun jima suna juya wa wannan Kasa tamu baya musamman Arewacin Nijeriya, kuma duk abin da suka jawowa Arewacin Nijeriya na juya baya yanzu Buhari shi ya zo yake yin su. Kullum sai a ce ba za a turo mai Arewa ba, ga shi kuwa jihohi biyar muna da mai, amma wadannan Jihohi da aka fada irin man ne fa Kasar Chadi take tonowa, irinsa ne Kamaru take tonowa, irin sa ne Nijar ke tonowa, haka Ghana.
Don me mu idan za a tono daga inda ake tono shi sai a ce man yana da wahalar tono, to wadannan Kasashen da suk tono wa kuma suke rayuwa da shi fa? Kai dan Nijeriya idan aka tono man nan ai amfaninka ne, sawa’un kana Kudu ne ko Arewa, Kana Musulmi ne Ko Kirista, amfaninmu ne karin ci gaban kasar mu ne, amma dai tun da muna da shi a tono shi mu yi amfani da shi. buhari ya gaba yana tono shi, Mombila ta fi shekara 30 tun a lokacin tana cin tsarin su Sardauna Allah da ikonsa aka yi wancan juyin mulki abin bai yi tasiri ba, zancen ya taso kamar zai yiwu lokacin da Gowon yana mulki, gama da yaki da aka sha yi, nan ya zama Allah bai sa an samu ci gaban abin ba. wadannan Gwmanatotci suka zo daga baya ko wanne ya fara, daga inda ake fara dakele abin daga wani bangare ne na Kasar nan tamu a ke dakile abin a bata shi da baki a lalata shi a wargaza shi.
Buhari ya zo ya fara abin nan ka’in da na’in, aka zo tashar jirigin ruwan nan ta Baro ka ga inda Buhari ya kama ta ka’in da na’in ga shi yau din nan ake zaton an bude ta, wanda shi ma wannan aikin ya fi shekara talatin duk wanda ya zo zai yi sai an tade shi, ‘Yar aduwa d ya zo ya ware kudi kan za a fara Allah ya yi ikonsa ya karbe shi, aka dauki wanda aka amince da shi wanda suka yi aiki tare shi kuma ya dauke kudin ya yi wani wurin da su kuma aka debi wasu kudin aka boye aikin kuma aka watsar, yau ga Shugabn Kasa Buhari yana fito da wannan aiki.
Ga kamfanin sarrafa karafa na Ajaokuta duk Afirka ko Kasar Masar ba ta fi mu injiniyoyi ba ta yadda za a iya kera abubuwa dama, amma Ajaokuta aka nakasta ta, ga mai girma Shugaban Kasa ya zo ya tayar da kokari a kanta. Bayan wannan kuma ga ayyuka na hanyyoyi jirgin kasa, inda aka sa su wurare daban-daban a Kudancin Nijeriya da Arewacin Nijeriya yanzu ana ta shimfida kwalta, ayyukan da masu sukan sa suka gaza yi.
Ga titi daga Maiduguri zuwa Knao, aikin da ya kai kusan shekara 25 a takaice da aka dakile shi ba a yi ba ga shi an fara, harkokin kasuwanci, harkokin noma duk an gyara su. Tabbasa Buhari shi ne mafita, domin daga ji an ce za a sayar da NNPC, mutumin da Kasar Amurka ta hana shi Biza sai ga shi ta ba shi,kuma a hankalce ba man ‘yan Nijeriya za a sayar ba ‘yan Nijeriya za a sayar. Wannan harataccen ciniki ne ake kokarin kulla shi, wanda da zarar an ba su cin hanci ko da biliyan-biliyan ne, su da aka sayar din za su ga kamar an ba su ne kyauta. Saboda haka ya kamata ‘yan Nijeriya mu farka bacci.
Don haka ina kira ga ‘yan Nijeriya musamman ‘yan kasuwa su sani ba mu da wani Shugaba idan ba Buhari ba, domin duk abin da zai yi idan y agama kudin nan kasuwa za su dawo, saboda haka mu zabi Buhari, an kishin Kasar da ba ma a Nijeriya ba har Afirka ana kimarsa da darajarsa har ma da duniya baki daya. Wannan mai amanar shi ya kamata mu sake zaba baki daya, Allah ya sa a yi zabe lafiya a gama lafiya, salamu alaikum.

Exit mobile version