Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga ministan ilimi, Malam Adamu Adamu da ya kawo karshen yajin aikin ASUU.
An ruwaito cewa shugaban ya bayyana haka ne a ranar Talata inda ya bayar da umarni ga ministan ilimin da ya sasanta abubuwan da ake tamaddama a kai cikin mako biyu sannan a kai masa rahoto.
A yau Talata shugaba Buharin ya tattauna da ma’aikatu da masu ruwa da tsaki wadanda ke da alaka da bangaren ilimi da za su iya warware tirka-tirkar yajin aikin.
Shugaban ya kira su ne domin ya samu karin bayani kan dalilin da ya sa wannan yajin aikin ya ki ci ya ki cinyewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp