Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nuna bacin ransa kan kashe jami’an tsaro na farin kaya na NSCDC bakwai da ‘yan bindiga suka yi a Jihar Kaduna.
An ruwaito cewa, an hallaka jami’an ne a yayin da suke kan gudanar da aikinsu na tabbatar da tsaro.
- Tinubu Zai Doke Atiku Da Obi A Zaben Shugaban Kasa – Danbazau
- Jam’iyyun APC Da NNPP Na Mayar Wa Da Juna Martani Kan Sabbin Masarautun Kano
Buhari a cikin sanarwar da hadiminsa, Garba Shehu ya fitar a yau Alhamis, ya danganta kisan, a matsayin babban lamari, inda kuma ya nuna bacin ransa kan rasa rayukansu a lokacin da suke kan kare rayukan ‘yan kasar nan.
Buhari ya kara da cewa, kashe su a lokacin da suke kan gudanar da aiki, ya zama tamkar sadaukar da kai ne wajen bai wa kasar nan kariya.
Shugaban ya kuma mika ta’aziyyarsa ga ‘yan uwa da abokan arziki na mamatan.
Buhari umarci jami’an sojin kasar nan, da su zakulo ‘yan bindigar da suka aikata wannan aika-aikar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp