Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya haddasa wa Nijeriya koma-bayan da sai an yi shekara 50 ba a murmure ba a tsawon mulkinsa na shekara 8.
Fayose ya bayyana hakan ne wata tattaunawa da gidan talabijin Channels a shirin harkokin siyasa na ranar Lahadi.
Tsohon gwamnan ya ce mummunan tsarin Buhari mara kyau ne ya jefa kasar nan cikin mawuyacin hali.
- Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Layin Dogo Da Kamfanin Sin Ya Gina A Legas
- Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Kar-ta-kwana Kan Haramtattun Gine-gine
Ya gargadi Shugaban kasa, Bola Tinubu ya dakatar da mummunan tsare-tsaren Buhari, domin sun jefa Nijeriya cikin koma-bayan da sai an shekara 50 ba a farfado ba.
Fayose ya siffanta gwamnatin Buhari a matsayin abun ladama, sannan kuma a yanzu ana dandana ukuban da gwamnatinsa ha haddasa ga ‘yan Nijeriya.
A cewar Fayose, kwazon Tinubu yana haifar da da mai ido. Ya ce babu wani tsafi da Shugaban Tinubu zai yi ya dawo da lamura daidai, domin gwamnatinsa ba ta wuce watanni tara ba a kan karagar mulki.
Fayose ya ce, “Wata tsohuwar ministan kudi ta ce bashi yana lakume kashi 83 na kudaden da Nijeriya ke samu.
“Idan aka danganta lamarin da wannan gwamnati wacce ta gaji dinbin bashi za a ga cewa tana iya bakin kokarinta,” in ji shi.
Idan dai za a iya tunawa Nijeriya tana fuskantar kalubale masu yawa da suka hada da hauhawar farashin kayayyaki, matsalar sauyin kudaden waje, tabarbarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa wanda ya samu asali tun lokacin da aka cire tallafin man fetur, inda a yanzu haka ake ta gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a kasar nan.