Wani abu mai tayar da hankali a bangaren gine-gine a Nijeriya a wannan lokacin yanzu wanda a lokutan-baya sai dai a ji labari dai-dai amma yanzu al’amarin ya zama ruwan dare, shi ne annobar rushewar gine-gine, wanda hakan ke nuna irin matsalar da bangaren gine-gine na Nijeriya ya shiga.
Rahotanni daga sassan kasar nan suna nuna yadda ake samun rugujewar gine-gine abin da ke kai ga asarar rayukar al’umma da dukiyoyin mutane da dama, mutane sun zura ido ga gwamnagti don ta samu musu mafita na yadda masu ruwa da tsaki da harkar gine-gine za su tabbatar da bin doka da oda a harkokinsu.
Zuwa yanzu rushewar gine-ginen da aka samu a baya ba mu ji labarin gwamnati ta dauki matakin hukunta masu hannu a kan faruwar lamarin ba, da kuma jami’an gwamnati wadanda su ke bayar da izinin yin gine-ginen da kaya marasa inganci.
Idan za a iya tunawa, a watan Satumba, mutum biyu sun mutu yayin da ma’aikata 4 suka makale a karkashin baraguzai a yayin da wani bene mai hawa 2 ya rushe a unguwar Oba Abiodun Oniru a yankin rukunin gidaje na Oniru, a Lekki ta Jihar Legas.
Yakamata ya yi a lura da cewa, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, LASEMA, ta bayyana cewa, gidaje 30 suka rushe a sassa daban-daban na Jihar Legas a tsakanin watan Janairu zuwa Yuli na 2022.
Kididdiga ta baya bayan nan, kamar yadda Babban Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, Dakta Femi Oke-Osanyitolu ya nuna, ya ce, daga cikin kiran gaggawa 973 da aka yi musu mafi yawa na rugujewar gine-gine ne, an kuma fi samun wadannan kiraye-kiraye na gaggawan ne daga karamar hukumar Alimosho inda aka samu gidaje 24 da suka ruguje gaba daya da gidaje 6 da wani bangare nasu ya ruguje da kuma wani gida da yake dab da rushewa.
Hakanan kuma, rahotanni daga kafafen watsa labarai na nuna cewa, akalla mutum 84 suka rasa rayukansu a cikin gidaje 18 da suka rushe a Jihar Legas a cikin shekara 2 da suka wuce.
Kusan mako 4 kenan da rushewar wani bene mai hawa 4 a yankin Bodija da ke Ibadan a Jihar Oyo sai kuma gashi wani bene mai hawa 2 ya sake rushewa a yankin da ake magana a daren ranar Lahadin da ta wuce.
A watan da ya gabata, wani bene mai hawa 4 ya rushe a Uyo, babbar birnin Jihar Akwa Ibom inda mutane da dama suka makale a cikin baraguzan ginin.
A watan Agusta kuma, wani mutum ya mutu bayan da wani bene mai tsawo ya rushe a garin Kano inda wasu da dama suka makale. An tabbatar da mutuwar mutum biyu a watan Agusta a yayin da wani bene mai hawa 3 ya rushe a garin Kubwa da ke yankin babban birnin tarayya Abuja.
A ra’ayin wannan jaridar, muna iya cewa, a halin yanzu muna fuskantar annobar rushewar gine-gine ne a kasar nan. Abin takaicin kuma shi ne, daga shekarar 1974 zuwa watan Yuli na shekarar 2021, kididdiga ta nuna cewa, gidaje 461 suka rushe a Nijeriya inda fiye da mutum 1,090 suka mutu wasu kuma suka rasa rayukansu.
A ‘yan shekarun nan an samu rushewar gini 295 a Jihar Legas, Abuja 16, Oyo, 16, Anambra 15, Kano 9, Ondo 10, Abia 9, Kwara 8, Ribers 8, Delta 8, Enugu 7, Ogun 7, Plateau 6, Kaduna 6, Edo 6, Imo 5, Osun 5, Benue 3, Adamawa 3, a Jihar Ebonyi kuma guda 3. An samu rushewar gini 2 a Neja, Kebbi 2, Ekiti 2, Cross Riber 2, Sokoto 1, Bauchi 1, Akwa-Ibom, Kogi 1, Jihar Katsina kuma gini 1.
Masana sun dora alhakin yawan rushewar gine-ginen kan yadda ake amfani da kayan aiki marasa inganci da rashin bin ainihin taswirar da aka samar don ginin da kuma rashin yin binciken da ya kamata a a kan yanayin kasar da za a yi ginin a kai, bugu da kari kuma amfani da baragurbin ma’aikata wadanda ba su da kwarewar da ta kamata na haifar da irin wannan matsalar ta rushewar gine-gine.
Muna kira da gwamnati da a tabbatar da an gano tare da hukunta dukkan kwararrun da ke da hannu a gidajen da suka rushe da wadanda suka zuba jari a harkar ginin da ya rushe, wannan zai zama darasi ga masu daukar aikin da ya rataya a kan da muhimmanci.
Ya kuma kamata gwamnati ta tabbatar da bin dokoki da ka’idojin da ke tattare da gine-gine a Nijeriya tare da hukunta duk wani jami’in da aka samu yana sakosako da ayyukansa wanda hakan ya kai ga rushewar gini a fadin tarayyar Nijeriya.