• English
  • Business News
Wednesday, October 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Rogo A Duk Shekara A Nijeriya Ya Kai  Tan Miliyan 300,000, Cewar Masana

by Abubakar Abba
2 years ago
Rogo

Wasu masana a fannin noman Rogo a kasar nan, sun bayyana cewa,  bukatar da ake da ita ta Rogo don sarrafa shi zuwa sauran nau’ukan abinci ya kai tan miliyan  300,000 a duk shekara.

Sun bayyana hakan ne a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki a fannin da suka gudanar a babban birinin tarayyar Abuja.

  • Rikicin Nijar: Tinubu Ya Aika Janar Abdulsalami, Sultan Na Sokoto Zuwa Yamai
  • Chelsea Ta Dauki Mai Tsaron Raga Daga Brighton

A cewarsu,  samar da shi ya kai kasa da tan 10,000 tonnes; haka ana kara bukatar Rogon wajen sarrafa magunguna da suka kai sama da tan 350,000.

Sun kara da cewa, karin bukatar da ake da ita ta man da ake samu da ake kiransa a turance ethanol da ake yin amfani da shi wajen girki da kuma wanda ake sanya wa ababen hawa wato a kasar nan ya karu zuwa lita biliyan daya.

“Samar  da shi ya kai kasa da tan 10,000 tonnes; haka ana kara bukatar Rogon wajen sarrafa magunguna da suka kai sama da tan 350,000.”

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

Masanan sun ci gaba da cewa,  sama da kadada miliyan 24 ake noman Rogo a kasashe 106, inda suka bayyana cewa,  Nijeriya ke a kan gaba wajen samar da shi.

Kazalika, a cewarsu, amfanin  ya kasance daya daga cikin amfanin gona da ke kara karfafa tattalin arzikin duniya.

Sun sanar da cewa, bincike ya nuna cewa, Nijeriya a matsayinta ce take kan gaba wajen noman Rogo, inda  suka ce, kasar na samar da kimanin tan miliyan 53 na Rogo a duk shekarar.

Sun kara da cewa, kasr na kuma  samar da akalla tan  7.7 ako wacce kadada daya.

Sun  bayyana cewa, bisa wata kididdigar da aka fitar a kwnan baya, ta bayyana cewa, daga cikin tan miliyan 53 na Rogon da ake noma wa a Nijeriya a duk shekara.

Kazalika sun bayyana cewa, sama da kashi 90 a cikin dari  ana sarrafa Rogon zuwa sauran wasu nau’ukan abinci, inda kuma masana’antun da ke sarrafa shi a kasar suke ci gaba da nuna bukatarsa.

Hakazalika, fannin na noman Rogon ya taimaka wajen samar wa da  miliyoyin ‘yan Nijeriya aikin yi idan kuma aka inganta fannin, zai samar fiye da hakan.

“Kashi 90 a cikin dari  ana sarrafa Rogon zuwa sauran wasu nau’ukan abinci, inda kuma masana’antun da ke sarrafa shi a kasar suke ci gaba da nuna bukatarsa.”

Wasu daga cikin manoman da suka halarci taron na masu ruwa da tsaki a fannin na noman Rogon a kasar nan sun bayyana cewa, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara bunkasa fannin ganin cewa, fanni ne da ke kara  bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

 “Nijeriya ta kasance a kan gaba wajen fitar da Rogo zuwa kasar waje, inda kuma hakan ke kara habaka mata kudaden ta ajiya a asusun kasar waje.”

Sun kuna nuna bacin ransu akan yadda  Nijeriya ke shigo da Rogon da ya kai na sama da dala miliyan 600 a duk shekara.

“Fannin na noman Rogon a kasar nan sun bayyana cewa, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara bunkasa fannin ganin cewa, fanni ne da ke kara  bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.”

Sun yi nuni da cewa, akwai matukar bukatar a samo masu zuba dimbin jarinsu a fannin, musamman don a cike gibin bukatar da ake da shi da kuma tura shi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

October 11, 2025
Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
Noma Da Kiwo

Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

October 11, 2025
Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara
Noma Da Kiwo

Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

October 11, 2025
Next Post
Majalisa Ta Ki Amincewa Da Shirin Tinubu Na Daukar Matakin Soji A Kan Nijar

Majalisa Ta Ki Amincewa Da Shirin Tinubu Na Daukar Matakin Soji A Kan Nijar

LABARAI MASU NASABA

Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar

Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar

October 15, 2025
Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

October 15, 2025
Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

October 15, 2025
Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

October 15, 2025
Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

October 15, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

October 15, 2025
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci

Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu

October 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako

October 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

‘Yansanda Sun Kama Mutum 105, Sun Ƙwato Ƙwayoyi Sama Da 5,000 A Jigawa

October 15, 2025
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara

October 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.