A ‘yan shekaraun nan, Nijeriya ta ci gaba da fuskantar abubuwa marasa dadi na tashin hankali na hare-hare a makarantunmu, makarantu da ya kamata su kasance wuri na samar da matasan da za su zama jagororin al’umma a nan gaba, a yanzu sun zama wurare da ake zaune cikin tsoro da zullumi da tashin hankali.
A yayin da muke nazarin kididdgar da wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Safe the Children’ ta fitar, ya zama dole a matsayinmu na kasa mu gaggauta samar da hanyoyin kare makarantunmu daga ayyukan masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga.
- Ana Zura Ido Kan Yadda Amurka Za Ta Ki Raba-gari Da Kasar Sin
- Dan Daba Ya Yi Wa Dan Jarida Dukan Tsiya A Cikin Gidan Gwamnatin Adamawa
Rahoton kungiyar ya nuna cewa, tun daga lokacin da aka sace ‘yan makarantan nan su 276 a garin Chibok da ke Jihar Borno a shekarar 2014, ‘yan makaranta fiye da 1,680 aka yi garkuwa da su. Wannan lamari na tayar da hankali, don kuwa ‘yan makaranta 180 suka rasa rayukansu yayin da 90 suka ji raunuka daban-daban a hare-haren da aka kai wa makarantu a fadin tarayyar Nijeriya abin da ya zama wata barazana da kuma tashin hankali ga sauran dalibai da iyayensu.
Haka kuma, bayani ya nuna cewa, an yi garkuwa da malaman makarantu 60 yayin da malamai 14 suka rasa rayukansu a hare-haren da aka kai makarantun an kuma lalata makarantu 25 a sassan Nijeriya.
A matsayinmu na gidan jarida, ra’ayinmu a nan shi ne, wadannan ba wai suna matsayin kididdiga ba ne kawai sun zama wani lamari da ke dakushe mafarkin matasanmu na zama wani abu a nan gaba, yana kuma lalata ginshiki da fatan da ake da shi ta bunkasar tsarin karatun Nijeriya gaba daya.
An kaddamar da wannan kungiyar ta ‘Safe Schools Initiatibes’ ce bayan da aka sace ‘yan matan makarantar Chibok a shekarar 2014 da mufin tabbatar da kariya ga makarantunmu. Wannan shiri yana samun tallafi da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar ‘yan kasuwan Nijeriya da sauran kungiyoyi masu zaman kansu, sun kuma nemi a tabbatar da samar da yanayi da muhalli mai tsafta da dalibai za su yi karatu ba tare da barazana ko kuma tsoro ba.
An samar da fiye da Dala Miliyan 30 a lokacin da aka kaddamar da shirin da nufin fitar da tsarin kare makarantu don samar da matasa da zamu iya alfahari da su a jagorancin kasar nan a nan gaba.
Amma kuma wannan mafarki da fata na kungiyar ‘Safe schools’ bai samu cika ba don kuwa an ci gaba da kai hare-hare a makarantu musamman a Arewancin Nijeriya, abin da yake ci gaba da sanya tsoro a kan yiyuwar samar da gyaran da ake bukata a bangaren makarantunmu.
Karuwar hare-haren da kuma garkuwa da ‘yan makaranta da ake ci gaba da yi ya jefa tsoro a zukatan dalibai da iyayensu gaba daya.
Tambaya mai muhimmanci da ya kamata mu yi a wannan lokacin ita ce wai shin menene matsayin kungiyar ‘Safe Schools Initiatibe’ kuma ina fiye da Dala miliyan 30 da aka tara a lokacin kaddamar da kungiyar suka shiga?
Binciken da jaridar nan ta yi kwanakin baya ya nuna cewa, shekaru da dama da kaddamar da shirin ‘Safe Schools Initiatibe’ har zuwa yanzu wasu jihohi da dama basu amfana daga wannan asusun ba, haka kuma basu amfana da shirin kungiyar na kare makarantu ba.
Wannan wani abu ne da ya kamata ya tayar da hankali al’umma da dama musamman ganin kungiyar da ke da alhakin samar da kariya ga makarantumu ta gaza cika alkawarinta. Ana ci gaba da kai hare-hare a makarantunmu babu kakkautawa, a kan haka yana da matukar muhimmanci mu mika ayar tambaya ga masu tafiyar da kungiyar, na su bamu cikakkiyar bayanai na yadda aka sarrafa kudaden da aka tara don al’umma su san yadda aka kashe su.
Barnar da wannan lamari ya yi ga matsalar tsaro yana da matukar girma musamman ganin Nijeriya na da dimbin yara da ke gararamba a kan titi basa zuwa makaranta, an kiyasta cewa, yara fiye da kashi 12.4 na yara wadanda basa zuwa makaranta suna yankin Afrika ta yamnma ne.
Matsalar tsaro ta hana wadanna yara zuwa makaranta, an hana su damar bayar da nasu gudummawarsu ga bunkasar al’ummar yankinsu da kasar su gaba daya.
Ba wai muna jinjina matsalar kawai ba ne, ya kamata mu dauki mataki na kare makarantun don samar wa yaranmu rayuwa nagari.
Muna kira da a gudanar da bincike na musamman a kan yadda aka gudanar da kungiyar ‘Safe Schools’ don gano yadda aka kashe kudaden da aka tara, muna kuma bayar da shawara a tabbatar da wata kungiya ce mai zaman kanta za ta gudanar da binciken don kauce wa zargi da tabbatar da gaskiya.
Dole gwamnati ta muhimmantar da samar da tsaro a makarantumu ta hanyar samar da karin jami’an tsaro a makarantu, a kuma karfafa samar da bayanan sirri da za su kai ga tarwatsa shirin ‘yan ta’adda tare da aikawa da gargadi a duk lokacin da aka samu wasu bayanai da ke nuna akwai wata matsala.
Al’umma na da rawar da za su taka wajen tabbatar da tsaron makarantumu, ya kamata su shiga a dama da su wajen kare makarantunmu ta hanyar bayar da bayanan sirri ga jami’an tsaro da za su kai ga dakile ayyukan ‘yan ta’adda a yankunanmu.
Ya kamata dalibai da malamai da suka fada hannun ‘yan ta’adda su samu tallafi na musamman na kwararru da zai taimaka musu su farfado daga tashin hankalin da suka fuskanta.
Abin takaicin a ra’ayinmu shi ne labarin dalibar makarantar Chibok da aka ceto kwanan nan, inda ta nemi a mayar da ita ga ‘yan ta’addan da suka kama ta. Wannan yana nuna cikakkiyar halin da kasarmu ke ciki ne.
A kan haka muke kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi su muhimmantar da lamarin tsaron makarantumu, ta hanyar samar da kudade da kayan aiki ga jami’an tsaro don yin haka tamkar kare kasa ce baki daya. Lokaci ya yi da zamu tabbatar da kare makarantun da kuma kare mutuncinmu.