A daidai lokacin dababban zaben kasa na shekarar 2023 ke karatowa, kusan saura wata biyar a halin yanzu. Ana sa ran zuwa yanzu dukkan abubuwan da suka shafi harkar zaben duk an kammala su don tabbatar da gudanar da zaben tare da fuskanta da kuma warware dukkan matsalolin da za su iya tasowa daga zabukan daza a yi.
A kan wannan nemuke matukar damuwa a bisa yadda zuwa yanzu gwamnatin tarayya ba ta samar da kudade ba ga kotuna sauraron kararrakin zaben da ka iya tasowa a zaben 2023, musamman ganin tuni aka kafa kotunana fadin tarayyar kasar nan gaba daya.
- Firaministan Habasha Ya Kaddamar Da Dakin Adana Kayan Kimiyya Da Fasaha Da Kasar Sin Ta Samar
- Tinubu Ya Dawo Nijeriya Bayan Shafe Kwanaki 12 A Birtaniya
Bayanin da muka samu ya nuna cewa, shirye-shiryen da suka shafi horas da manyan masu shari’a, shugabannin kotuna na musamman da sauran ma’aikatan kotunan ya tsaya saboda rashin isasashen kudade wanda gwamnati ta kasa samarwa.
Shugaban Kotun Daukaka Kara, ya yi wannan koken inda ya kara da cewa, kotunan musammnan da ake da su a halin yanzu duk sun cinye kudaden da hukumar ta tanada.
Ya kuma sanar da cewa, a halin yanzu babu wani kudi a asusun hukumar da za a iya kafawa tare da gudanar da kotunan sauraron kararrakin zaben. Kotunan sauraron korafe-korafen zabe na da muhimmanci a harkokin gudanar da zabe, su ne ke sauraro korafe-korafen da ke tasowa tun daga lokacin da ake tantance masu kada kuri’a har zuwa lokacin daza a sanar da wanda ya lashe zaben gaba daya.
Hakan na da matukar muhimmanci don kare aukuwar rikice-rikicen da ka iya tasowa bayan zabe tare da tabbatar da cikakken zaman lafiya a kasa. Hakki ne na Kotun Daukaka Kara kafa Kotunan sauraron kararrakin zabe, ana kuma kafa su ne tare da la’akari da tanade-tanaden sashi na 285 (2) na kundin tsarin mulkin shekarar1999 (kamar yadda aka yi wa sashi na 9 na dokar kwaskwarima a shekarar 2010).
A ka’ida, Kotun Daukaka Kara ta Tarayyya ce daga ita sai kotun koli a tsarin kotunan Nijeriya. Amma kuma Kotun Daukaka Kara ce ke tsara yadda za a gudanar da shari’un dauka kakara a tsarin shari’ar kasar nan, haka kuma hukumar kula da harkokin shari’a ce ke zabo masu shari’a a wadannan kotunan su mika wa shugaban kasa daga nan kuma majalisar Dattawa ta amince da su.
Dole masu shari’a na kotuna daukaka karar su zama suna da kwarewar gudanar da ayyukansun a Nijeriya sun kuma yi aiki a matsayin masu shari’a a Nijeriya na fiye da shekara 12.
Tsarin mulkin ya kuma tanadi cewa, masu shari’ar za su ajiye aiki in har suka kai shekara 65 a duniya. A saboda haka ya kamata a fahimci cewa, kotunan na da matukar muhimmanci a tsarin gudanar da harkokin dimokradiyya.
Kotunan na bayar da dama ga wanda yake da korafi ya tafi kai tsaye gaban kotun don mika korafinsa don neman a warware masa matsalolin da ya hango a yayin gudanar da zabukka.
Babu wani bangare na gwamnati da ke da irin wannan karfin, wannan alakar yana daga cikin zuciya da ginshikin harkar dimokradiyya. Yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa, yin cikakken shiri a dukkan harkokin rayuwa yana tattare ne da isasshen kudi na gudanar da harkokin lamarin.
A saboda haka samar da kudi na da muhimmanci in har ana son kotunan su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. A kan haka muna kira ga hukumomin da ke da ruwa da tsaki da su gaggauta samar da kudaden da suka kamata ga kotunan zabe don a samu nasarar da ya kamata a zaben 2023 da ke tafe.
Tabbatar da tsayayyiyar bangaren shari’a na da matukar muhimmanci ga kokarin tabbatar da aldaci da sahihin zabe a harkar dimokracdiyya, dole a tabbatar da ana yin adalci tare da ganin adalcin a bayyane, kuma hakan ga zai taba yiwu ba har sai an samar wa da bangaren shari’a isasshen kudaden gudanar da aiki.