Connect with us

Madubin Rayuwa

Bukukuwa Da Al’adun Kabilar Luo

Published

on

Kamar yadda a makon da ya gabata filin namu ya sada ku da mutanen kabilar ‘Luo’ dake yammacin Kasar kenya, Arewacin Yuganda, da kuma wajejen mara na yankin Tanzaniya, a wannan makon ma za mu dora ne a kan abubuwam da suka shafi bukukuwa na Luo da sauran harkokinsu na al’ada.

Kamar yadda muka bayyana a makon da ya gabata, su Mutanen Luo ko kuma a ce mutanen Joluo ko Jonagi, ko Onagi, in mutum daya ne a ce Jaluo ko Onagi Ko kuma Joramogi/Nyikwaramogi ma’anarsa magajin Ramogi, Kabila ce a yammacin Kasar Kenya, da kuma Arewacin Uganda, sai kuma wuraren Mara chan Arewacin Tanzaniya.

Suna daga cikin manya kabilu ma’abota yare don kuwa kama daga Kudancin Sudan, Kudancin Arewar Ethopia, Gabas da kuma Arewacin Uganda, Kudancin Yammacin Kenya da kuma Arewacin Gabashin Tanzaniya.

Da yawa daga cikin bikukkuna da al’adun mutanen luo sun zama tarihi ko kuma an chanza musu stari daga tsarin su na asali, saboda zuwan turawan mulkin mallaka da kuma shigowar addinin christanci.  Amma akwai bikukkunan da akan bi tsarin al’ada wurin yin su har a yau.

A misali,a yandu al’adar cire hakorin kasa, da zanen da akan zana a bayan yara mata da su sharan gjda da daddare duk sun zama tarihi.

Ba kamar sauran yarukan makwaftan luo ba,su basu taba saka yin kaciya a cikin al,’adar su ba abubuwa masu muhimmanci biki ne sai mutuwa a wurin su.

 

Akan yi  Bikin auren gargajiya kan gudana ne ta fiskoki da dama,a farko akan fara da Ayie ma’ana sunan abun kenan Ayie a inda ango da kansa ke kawo kudi a biya mahaifiyar amarya. Sai kuma na biyu, a kawo saniya wa mahaifin ta.  Bayan an gama kawo wannan sai kuma abun da ake kira Meko, kamar ace dauke amarya shi ne lokacin da ake dauko amarya zuwa gidan mijin ta,sai kuma daga karshe ayi yankan katuwar bujumi sai ayi biki.

Sai kuma bison mamaci,ba yan uwan mamaci kadai ke wannan bikin ba duka mutanen garin ke yi. Akan yi shi ne a garin luo ko a ina mutum ya ke zama dole a garin na luo za’a bisine shi, zuwa wurin biso dole ne akan ko wani dan garin na luo domin kuwa anan akan kara dankon zumunci har a kulla auratayya. Kwana hudu ake yi ana Bikin biso na mamaci namiji, ayi kwana uku wa mace. A bikin ana shan giya mai yawa tare da naman yankan da akeyi shi ma mai yawa domin a girmama mamaci.

Bayan yan koke koke, sai kuma a barke da bidiri duk bakin da suka zo a lokacin dan mutuwar za’a sauke su a kauyen mamacin.

 

A da chan akan yi bikin haihuwa, kuma shi abu mafi amfani a wannan biki shi ne gabatar da jaririn zuwa duniya.  Ana wannan biki ne bayan an haihu da kwana hudu in namiji ne, kwana uku kuma in diya mace ce.  Akwai aski da ake wa yaro wadda kakar yaro ta mace ne ke yi a inda ta kan samo rezar ta mai kafi tare da bawon kabewa wadda aka fafake aka cika da ruwan jike jike na magunguna dan wanka da tsaftace kan yaron.

Abun al’ajabin yana wurin bikin sa wa yaron suna inda akan bar wa iyayen yaro su suka da kansu. Sunayen akan ala kanta su da duniyar fatalwa inda akan alakanta sunan da lokaci na rana ko kuma lokaci na shekara.  A misali in aka haifi yaro lokacin fitowar rana zai ci sunan sa Okinyi in namiji ne ta mace kuma Akinyi. In kuma an haife shi bayan fitowar rana toh za’a kira yaro Atieno ko Otieno kaman yadda na fada a baya suna ne na yara mata da kuma yara maza.  In kuma lokacin ruwa ne  Mace da’a ce da ita Akumu namiji kuma okumu.  Haihuwan yan biyu kuma, aiki ne na mugayen fatalwa haka ma yaran da aka haifa kafun aure sunyi imani cewa fatalwa ne da zai kwace albarkan yaran da za’a haifa cikin aure kuma ya bata auren, dan haka ana bada yaran riko warin kakannin su ko kuma ma su kashe kafun shekara Biyar.

Tarihin siyasar Luo

A karkashin mulkin mallaka na britaniya, kabilar Luo basu taba kasancewa sun sami matsala ta kwace ko mallake filayensu ba kamar yadda ta kasance ga sauran kabilu na kenya, kabilar Luo ta kasance kabila da ta taka rawar gani a bangaren siyasar kenya

Wasu daga cikin yayan kassr da suka kasance a cikin sahun shuwagabanni daga zuwan turawan mulkin mallaka, da kuma bayan zuwan turawan sun hada da

Jaramogi Oginga Odinga

Ochieng Aneko

Tom Mboye

Robert Oluko

Raila Odinga

Har ila yau kuma akwai sanannun mutane kamar

Washington Jalang’o

Okumu, James Orengo, Obama(senior)-the late father of Barrack Obama, tsohon shugaban kasar America.

[10:36, 8/29/2018] Aisha Seyoji: Tattalin arziki da abinci

Bangaren mutanen Luo dake rayuwa a kauyuka, kamun kifi (suo)  a kogin Bictoria shine abu mafi muhimmanci wajen neman kudi. Akan yi amfani da kifayen a gargajiyance, yayinda kuma wasun musamman   nauyi’ikan Nile perch ake ketarewa dasu kasar europe da sauran kasashe, kifi da uguli sune abincin da akafi sani a wajen mutanen Luo, Noma musamman noman rake, da kuma Auduga yana tasiri sosai a wasu wajajen da kabilar luo ke rayuwa
Advertisement

labarai