Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta ce ta kama wasu bata-gari 104 da ake zargi da aikata laifuka a wurare daban-daban a fadin jihar yayin gudanar da bukukuwan Sallah da aka kammala.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Usaini Gumel, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya cewa, an kama wadanda ake zargin da muggan makamai masu launi daban-daban a lokacin bukukuwan.
- Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Shirin Dashen Bishiyoyi Miliyan Uku
- Za A Gyara Wuta A Inganta Lafiya Da Ilimi Da Kuɗin Tallafin Lantarkin Da Aka Janye – Ministan Labarai
Gumei ya ce, rundunar ta himmatu wajen tunkarar duk wasu bata-gari da masu daukar nauyinsu da ke kokarin kawo cikas a zaman lafiyan da ake samu a jihar.
Ya bayyana cewa, an samar da isassun matakan tsaro don tabbatar da zaman lafiya a ciki da wajen birnin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp