Connect with us

LABARAI

Burutai Ya Jinjina Wa Dakarun Da Suka Dakile Harin Monguno

Published

on

Shugaban rundunar sojin Nijeriya, Lt Tukur Yusuf Burutai(COAS) ya taya ofisoshi da mazajen rundunar soji dake Monguno saboda jarumtarsu da jajircewarsu dasuka tarwatsha mayakan Boko Haram/ISWAP wadanda suka kai hari Garin Na Monguno ajiya Asabar 13 Ga watan Yuni,2020. Shugaban Sojin Lt. Yusuf Burutai yayi matukar jin dadi da ganin yawan ‘yan boko haram din da aka kashe da kuma kayan makamansu da aka kwato da taimakon sojin sama. Ya kara karfafa musu gwiwa da cewa su zamo cikin shiri akodayaushe don dakile duk wata fargaba da ka’iya afkowa.
Sannan COAS Lt. Burutai ya umarci shugaban sojin na Monguno da yabi sako-sako na mafakar ‘yan Boko Haram din dake zagaye dasu, su tabbatar sun tarwatsa su, kuma basu samu daman kara kawo wani hari ba.
COAS Lt. Yusuf Burutai yayi amfani da wannan dama yana mai kai sako ga rundunar soji da mutanen dake Katsina, Sokoto da Zamfara cewa yana nan zuwa don ganin yayi maganin ‘yan ta’addan dasuka damu yankunan. Kuma ya kara jin dadi da nasarar da tsarin Operation ACCORD da HADARIN DAJI ke samu. Ya bukace su dasu kara kaimi akan aikin su.
Bayanai na yawan makaman boko haram din da aka kwace ko aka lalata zamu fade su a labarai na gaba.
SAGIR MUSA
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: