Tawagar Chelsea da ta yi sabon mai koyarwa Ɗabi Alonso, tana da dama irinta wasu ƙananan ƙungiyoyi da ba za su buga kowacce gasa ba ta ba nahiyar Turai bayan wasannin cikin gida.
Duk da cewa ƙungiyoyi tara ne za su halarci wasannin nahiyar Turai amma Chelsea ba ta samu shiga cikinsu ba saboda gaza taɓuka abin kirki a bara. Dalilin haka shugabannin ƙungiyar suka ɗauki matakin kawo gyara cikinta, inda suka fara da kawo sabon mai horarwa Ɗaɓi Alonso da ya riƙe ƙungiyoyin Bayer Leɓerkusen da Real Madrid a baya, sai dai bai samu damar da ta dace ba a Real Madrid hakan ya sa ya bar aiki da wuri.
A ƙoƙarin gyaran da take yi Chelsea ta sayi ƴan wasa da dama wasu daga cikinsu sun haɗa da: Marco Palestra daga Atalanta da Morgan Rogers wanda ya kafa tarihin ɗan wasan Ingila mafi tsada, da kuma Maɗence Lacroiɗ ɗan wasan baya daga Crystal Palace kuma ɗan Faransa. Har ila yau, Chelsea ta ɗauki tsofaffin ƴan wasa da suka haɗa da Denny Welbeck daga Brighton sai kuma Jordan Henderson daga Brentford bayan ƙarewar kwantaraginsa.
Chelsea ta fi kowacce ƙungiya a Premier matasan ƴan wasa waɗanda za su daɗe ana fafatawa da su, hakan ne ya sa shugabannin ƙungiyar suka ga ya kamata su sirka da tsofaffi, shi ne dalilin kawo Welbeck da Henderson. Da wannan ake hasashen cewa za su buga Premier ba tare da gajiyawa ba, ba tare da wata damuwa ta cewa ƴan wasansu za su gaji ba.
Ko Aston Ɓilla Za Ta Maimaita Ƙoƙarinta Na Bara?
Aston Ɓilla ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe na kofin Eufa Super Cup da PSG, amma ita ce gwarzuwar gasar UEFA Europa ta 2026, kuma ta samu nasarar ne bayan doke SC Freiburg da ci 3-0. Ta kuma kammala gasar Premier da ta gabata a mataki na huɗu a saman Liɓerpool da tazarar maki biyar.
Unai Emery, kociyan ƙungiyar, wanda ya koma a watan Nuwamban shekara ta
2022 ya yi ƙoƙari a tawagar amma a wannan kakar da ta gabata ce ya taka muhimmiyar rawar gani. Aston Ɓilla tana da zaƙaƙuran ƴanwasa matasa da mafi yawansu ke tsakanin shekarun 21 zuwa 31. Duk da cewa ta sayar da ɗaya daga cikin mafiya ƙwazo a tawagar a bara Morgan Rogers, amma ta ɗauki Johan Manzambi ɗan Switzerland daga Freiburg da Jao Gomez na Brazil daga Wolɓes, ta kuma ɗauki aron ɗan wasan Argentina da ke buga wasa a Chelsea Alejandro Garnacho. Duka waɗannan na cikin abubuwan da ake kallon za su bai wa tawagar ta Unai Emery damar taka rawar gani da ɗorawa daga inda ta tsaya a ƙoƙarin da ta yi a bara.














