Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich Harry Kane ya zama dan wasan kasar Ingila na farko da ya lashe kyautar Ballon d’Or tun bayan da Michael Owen wanda ya lashe a shekarar 200, Kane ya karbi kyautar a wani gagarumin biki da aka shirya a Palladium Theater dake birnin Landan a ranar Litinin, dan wasan gaban mai shekara 33 shi ne dan Ingila na biyar da ya lashe kyautar a jimilla, sauran sun hada da Stanley Matthews a shekarar 1956, Bobby Charlton a shekarar 1966 da Kebin Keegan wanda ya lashe a shekarun 1978 da 1979.
Dan wasan Barcelona da Spaniya Lamine Yamal ya zo na biyu, yayin da dan wasan gaba na Real Madrid da Faransa Kylian Mbappe ya kare a matsayi na uku.
Kane ya zura kwallaye 61 a wasanni 51 da ya buga wa kungiyar a kakar wasan da ta gabata, wanda shi ne mafi yawan kwallaye da wani dan wasan Bayern ya taba zurawa a kakar wasa daya a tarihin kungiyar, a jimilla ya jefa kwallaye 73 idan aka hada da wasannnin kasa da kasa da ya wakilci kasar Ingila, hakazalika Kane ya taimaka wajen jefa kwallo 8 a wasanni 65 da ya buga.
Lionel Messi ne kadai a tarihi da ya taba zura kwallaye fiye da wadanda Kane ya zura a bara, duk da cewar Kane bai samu nasarar lashe manyan kofuna a bana da suka hada da Kofin Duniya da kuma gasar Zakarun Turai ba, amma ya taimaka wa Bayern Munich wajen lashe gasar Bundesliga da kofin kalubale na DFK.
Kyaftin din na tawagar Three Lions ya zama dan wasan Bayern na farko da ya lashe kyautar Ballon d’Or tun bayan KarlHeinz Rummenigge ya lashe a shekarar 1981.
Shi ne dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar Bundesliga a kakar da ta gabata inda ya jefa kwallaye 36, hakazalika ya jefa kwallaye 14 a gasar Zakarun Turai, sai kuma gasar cin kofin Jamus na DFK inda ya zura kwallaye 10, ciki har da kwallaye uku rigis da ya zura a wasan da suka doke Stuttgart da ci 3-0 a wasan karshe na gasar.













