Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home FITATTUN MATA

Chinedum Babalola: Farfesar Harhada Maguna Ta Farko A Jami’ar Ibadan

by Khalid Idris Doya
January 1, 2021
in FITATTUN MATA
3 min read
Chinedum Babalola
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ko-kun-san?

 

samndaads

Chinedum Babalola ita ce mace ta farko da ta fara zama Farfesar harhada maguna kuma kwararriya a fannin a jami’ar Ibadan?

A yau filin namu na dauke da tarihin wata fitacciyar farfesa a fannan kimiyyar hada maguna (Parmacy) a Nijeriya wacce ta samu nasarar cimma muhimman matakai, kana dumbin dalibai da malamai yanzu haka suna koyi tare da amfana da makaloli da koyarwarta.

Cikakken sunanta shine Chinedum Peace Babalola, kwararriyar masaniyar kimiyyar hada magunguna ce. Ita ce farfesa mace ta farko a sashin hada maguna ta jami’ar Ibadan. Kuma ita ce mace ta biyu a Nijeriya da suka fara zama farfesar hada maguna. Ita ce mukaddashiyar shugaban jami’ar Chrisland da ke Nijeriya.

Ta samu shaidar digirinta a fannin hada maguna a shekarar 1983, ta kuma yi digiri dinta na biyu kimiyyar hada maguna a shekarar 1987 sannan ta yi digiri na uku a fannin kimiyyar hada maguna a 1997 a jami’ar Ife, wanda yanzu ake kira jami’ar Obafemi Awolowo.

Ta samu nasarar cin kyautar karatu ta bankin duniya da hadin guiwar NUC ga ma’aikata wacce ta samu damar zurfafa karatu a jami’ar British Columbia daga 1994 da 1995.

A 2012, Chinedum ta samu shaidar wani diploma kan wani horo na musamman kan hada maguna (IPAT) wanda hadaka ne da makarantar Kilimanjoro school of Pharmacy da ke Tanzania da kuma jami’ar Purdue da ke Amurka. Ta samu shaidar Dakta a fannin hada maguna (PharmD) a jami’ar Benin a 2019.

Ayyukanta:

Chinedum Babalola ta fara aikinta ne a matsayin karamar malamar jama’a a jami’ar Obafemi Awolowo a 1985. A shekarar 1994, ta koma jami’ar British Columbia, wanda hakan ya bada damar zama malama mai daraja ta 1 a nan jami’ar Obafemi tsangayar koyar da ilimin kimiyyar hada maguna, daga baya ta koma aiki jami’ar Ibadan a matsayin babbar Malama a 1998. Kama-kama har zuwa lokacin da ta zama mace ta farko da ta fara zama Farfesar sashin hada maguna a jami’ar ta Ibadan a watan Oktoban 2006.

An nada farfesa Babalola a matsayin mukaddashiyar shugaban jami’ar Chrisland. Ta kasance mace ta farko da ta fara rike mukamin shugaban tsangayar kimiyyar hada maguna (Dean) a jami’ar Ibadan daga 2013 zuwa 2017, ta kuma yi aiki a matsayin mai dafawa a jami’ar Olabisi Onabanjo dukka a fannin hada maguna. Ta rike mukamin Darakta na sashin ilimin komai da ruwanka sau biyu daga 2005 zuwa 2010 a jami’ar Ibadan. Ita ce kwararriyar masaniyar hada maguna mace ta farko da aka nada a matsayin babban mai bada shawara kuma kwararriya a asibitin Nijeriya, ta kwalejin asibitin jami’a (UCH) da ke Ibadan.

Karin shahararta:

Farfesa ta fi maida hankali kan bincike magunan da za su taimaka wa mutum (dan adam), magunan da suka dace ake amfani da su a asibiti, da kuma wadanda za a ke baiwa marasa lafiya PK/PD, da kuma kasance mai zurfafa bincike kan cutar Sikila da Kansa. Ta wallafa wani littafi wanda ke kunshe da hanyoyin kyautata bada maguna ga marasa lafiya a fadin Afrika ta kuma zurfafa tunaninta kan magunan cutar Maleriya, da sauran fannoni daban-daban da ta samu cimma nasarori a kai.

Ta amshi lambobin yabo da daman gaske a rayuwarta musamman kan wacce ta bada gudunmawa da himma wajen kyautata hada maguna da zurfafa ilimi a fannin, wacce ta samu yin zarra matuka gaya a fannin hada magunguna a Nijeriya da ma Afrika.

Ta samu zarra sosai wacce a yanzu haka dumbin mata ke koyi da rawar da ta taka da salon koyarwarta, dalibai da dama ciki har da masu neman digiri na uku ke karkashin sanya idonta.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamna Buni: Ina Aka Fito Kuma Ina Aka Nufa? 

Next Post

Matsalolin Da Ke Biyo Bayan Zubar Da Ciki Ko Barin Ciki

RelatedPosts

Yesufu

@AishaYesufu: Shahararriyar ‘Yar Gwagwamarya A Nijeriya

by Khalid Idris Doya
4 weeks ago
0

Ko-kun-san……. Aisha Yesufu ta kasance ‘yar gwagwarmar nema wa al’ummar...

Halima Aliko Dangote: Jarumar Da Ke kokarin Bin Sawun Babanta

Halima Aliko Dangote: Jarumar Da Ke kokarin Bin Sawun Babanta

by Khalid Idris Doya
1 month ago
0

Ko-kun-san… Halima Aliko Dangote ita ce diya ta biyu a...

Jaruma

Sharon Ikeazor: Jaruma Mai Hankoron Nema Wa Mata Damammaki

by Khalid Idris Doya
1 month ago
0

Ko-kun-san….. Sharon Ikeazo, ita ce Minista a mukarraban shugaban kasa...

Next Post
Zubar Da Ciki

Matsalolin Da Ke Biyo Bayan Zubar Da Ciki Ko Barin Ciki

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version