A yau Talata, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gabatar da rahoton ayyukan gwamnati a taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, wanda ya nuna cewa, da ma a farkon bara, kasar Sin ta sanya burin samun karuwar ma’aunin tattalin arizki na GDP ta kashi 5%, da samar da karin guraben aikin yi kimanin miliyan 12, sa’an nan an ga yadda kasar ta cika burinta, inda a karshen bara, karuwar GDPn ta ta kai kashi 5.2%, gami da samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 12 da dubu 440.
Alkaluma na sauran fannoni su ma sun shaida cewa, tattalin arzikin kasar na ta karuwa cikin wani yanayi na daidaituwa, kana kasar ta cimma dukkan burikan da ta sanya gaba a bara. Wannan albishiri ne ga mutanen kasar Sin, kana labari mai kyau ne ga jama’ar kasashen Afirka.
Ko me ya sa na fadi haka? Saboda da farko, a matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arizki ta biyu a duniya, yadda kasar Sin ke iya kiyaye karuwar tattalin arizkinta yadda take bukata, da tabbatar da dorewar manufofinta na raya kasa, wani abu ne mai kyau, wanda ke haifar da yanayi na tabbas ga tattalin arzikin duniya, da karfafa gwiwar dimbin abokan hulda na kasar Sin, musamman ma kasashe masu tasowa.
Ba kamar wata babbar kasa ba, wadda ta dinga kara ruwan da ake karba kan kudin rance a bankuna, lamarin da ya haddasa hauhawar farashin kayayyaki mai tsanani a kasashen Afirka. Misali, a kasar Najeriya, tun daga watan Janairun shekarar 2022, darajar Naira kan dalar Amurka ta ragu da kashi 74%. Sakamakon haka, iyalin da ke iya kai yara zuwa jami’a wasu shekaru 2 da suka wuce, yanzu sai ya ga yana fama da yunwa. Abin takaici ne ganin yadda babbar kasar ta ki sauke nauyin dake rataya a wuyanta.
Sa’an nan, dalili na biyu, shi ne ci gaban kasar Sin ya kan haifar da ci gaba a kasashen Afirka.
Kasar Sin kawar kasashen Afirka ce wadda ta fi yin ciniki da su. Kana ta kiyaye wannan matsayi cikin shekaru 15 da suka wuce. Ban da haka, kasar Sin tana kan gaba a cikin kasashe masu tasowa, ta fuskar yawan jarin da ake zubawa kasashen Afirka. Ma iya cewa, alakar hadin kai mai karfi ta riga ta hada makomar kasar Sin da kasashen Afirka waje guda.
Bari in dauki manufar raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba a matsayin misali. Wannan manufa tana cikin manyan tsare-tsaren raya kasa na kasar Sin. Kana rahoton ayyukan gwamnatin kasar ya nuna cewa, karfin kasar na samar da wutar lantarki ta makamashin da ake iya sabuntawa ya wuce karfinta na samar da wuta ta makamashin gargajiya a karon farko a shekarar 2023, inda yawan sabbin tashoshin samar da wutar lantarki da makamashi masu tsabta da ta kafa cikin shekarar ya kai fiye da rabin adadin sabbin tashoshin na duk duniya.
Ko da yake kasar Sin ta samu ci gaba a wannan fanni, amma ko za ta manta da taimakon kasashen Afirka?
Ba zai yiwu ba. Kasar Sin ta farko ce daga cikin manyan kasashen da suka kulla yarjejeniyar hadin kai ta fuskar tinkarar sauyin yanayi tare da nahiyar Afirka, wanda ya aiwatar da daruruwan ayyukan samar da wutar lantarki da makamashi mai tsabta da tsare-tsaren jigilar wutar lantarki a kasashen Afirka, irinsu tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Zungeru dake Najeriya, da tashar samar da wutar lantarki ta karfin iska ta De Aar dake kasar Afirka ta Kudu, da tashar samar da wuta ta zafin rana ta Garissa dake Kenya, da dai makamantansu.
Zan ba da wani misali na daban. Cikin rahoton ayyukan gwamnati da kasar Sin ta gabatar a wannan karo, an ambaci manufar kasar ta raya tattalin arziki mai alaka da fasahar sadarwa ta zamani. To, a wannan fanni ma, ci gaban kasar Sin shi ma ya haifar da ci gaba na bai daya a nahiyar Afirka.
Stephanie Arnold, masaniya ce dake aiki a jami’ar Bologna ta kasar Italiya. Ta rubuta wani bayani a kwanan nan, inda ta ce tun daga shekarar 2010 har zuwa ta 2023, yawan mutanen kasashen Afirka masu yin amfani da hidimar fasahar sadarwa ta 3G ya karu daga kashi 22% zuwa kashi 83%, kana masu yin amfani da Mobile Broadband wato wayoyin sadarwa na tafi-da-gidanka sun karu daga kasa da kashi 2% zuwa kashi 48%. A cewarsa, “kasashen Afirka sun samu ci gaba sosai, kana kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a ciki.” Saboda a kalla kasashe 38 dake nahiyar Afirka sun zabi kamfanonin kasar Sin a matsayin abokan hadin gwiwa, a kokarinsu na gina wayoyin aika sako ta haske, da cibiyoyin sadarwa, da sauran kayayyakin more rayuwa, gami da horar da ma’aikata masu fasaha.
Ta hakan muna iya ganin yadda ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a sa’i daya ya zama dama ga kasashen Afirka na raya tattalin arizkin kansu.
Masu iya magana su kan ce, “ Tafiya mutum daya kadai na da sauri, amma tafiya tare da abokai za ta kai wuri mai nisa”. Ina sa ran ganin abokai na kasashen Afirka da kasar Sin, da suke tafiya tare kan turbar samun ci gaba, su isa wurin da suka dosa, komai nisansa. (Bello Wang)