Connect with us

MANYAN LABARAI

Cigaba Da Kulle Makarantu: Abin Da Ya Sa Kwamishinonin Jihohi Suka Goyi Bayan Gwamnati

Published

on

…Majalisar Wakilai Ta Yi Watsi Da Hujjojinsu

Kwamishinonin Ilimi a jihohin Arewa 19 sun ba da goyon baya ga dakatar da sake bude makarantu tun bayan da samu barkewar cutar Korona da Gwamnatin Tarayya ta yi umarni.

Kwamishinonin sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a jihar Kaduna a ranar Asabar, bayan wani taron tattaunawa da suka yi don sake bude makarantu da sauran batutuwan da suka shafi inganta fannin ilimi.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Kwamishinan ilim na Kaduna, Dakta Shehu Makarfi, wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar Hadin gwiwar shirin musayar Makarantun jihohin Arewa.

Taron ya samu halartar kwamishinoni 13 daga cikin jihohin Arewa 19, da suka hada da; Kaduna, Bauchi, Gombe, Neja, Nasarawa, Adamawa, Taraba, Kogi, Kwara, Katsina, Kano, Borno da kuma Jigawa.

Haka zalika, Kwamishinonin sun yaba wa Ministan Ilimi, Adamu Adamu, saboda jajircewarsa wajen yin tsayin daka game da nuna rashin amincewarsa ga sake bude makarantu tare da yin alkawarin ba da cikakken goyon baya.

A cewar su, batun daukar matakin rufe makarantu idan aka yi la’akari da yadda cutar Korona ke kara yaduwa a fadin kasar nan, wani mataki ne da ya dace domin ganin an tabbatar yara sun zauna lafiya, har zuwa lokacin da za’a gamsu rabuwa da cutar.

Saboda haka, mun yanke shawara amincewa da sake bude makarantu lokacin da aka tabbatar da babu wani hadari, sannan idan jihohi suka bi ka’idodin suka dace na yakar Koronan kamar yadda hukumar taki da cutar NCDC ta shimfida.

“Za mu shiga cikin aikin gudanar da Jarrabawar Sakandare ta Makarantar Afirka ta Yamma (WAEC), da sauran jarrabawa ne kawai idan an tabbatar da rashin wani hadari kan sake bude makarantun, da kuma lokacin da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta tsara,” a cewarsu.

Kwamishinonin, sun kuma yanke shawarar gudanar da cikakken bincike game da makarantu don tantance matsayin rashin tsaro kan sake budewar da kuma gabatar da sahihin rahoto ga gwamnonin nasu.

“Kayayyakin more rayuwa na makarantu da suka hada da kamar su lalatattun makarantu, dakunan kwanan dalibai, matattarar ruwa mai kyau, kayan aikin tsabta, gami da kayan wanke hannu da tsaro, wadannan abubuwa ne masu matukar mahimmanci kuma ya kamata a inganta su.

“Haka zalika kuma, za mu gudanar da ayyuka a makarantu, kamar su share dazuzzukan makarantun da ciyawa, da kuma kewaye su don tallafawa koyo da kuma tabbatar da tsaro lokacin da makarantu suka fara aiki,” in ji su.

Duk da haka, sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tallafawa jihohi wajen sanya matakan tsaro a wuraren da suka dace a yain sake bude makarantun.

A wani bangaren kuma majalisar wakilai ta yi watsi da shirin gwanatin tarayya na dakatar da shirin bude makarantu don dalibai ‘yan ajin karshe su zana jaraba kamamla karatu.

Kwamitin majalisar mai kula da tsarin ilimin farko, ‘Basic Education and Serbices’ ta soki eanna shawarar na hana dalibai zana jarabarwar WAEC na shekarar 2019/2020. An dai kulle makarantun ne saboda dakile yaduwau cutar corona.

A farkon watan Yuni ne kwamitin shugaban kasa akan cutar korona ta bayyana cewa, a halin yanzu ana iya komawa makarantu daki-daki ta yadda dalibai dake aji 6 na makaranyun firamare da kuma ‘yan aji 3 na karamar sakandire da kuma dalibai ‘yan aji uku na manyan makarantun sakandire za su iya komawa don zana jarabawar kammala karatunsu.

A martaninsa, Shugaban kwamitin, Farfesa Julius Ihonbbere, ya nuna rshin jin dadinsa akan shawarar gwamnnati na hana yara zana jarabawar, ya ce, bai kamata a soke jarabawar “WASSCE” ba.
Advertisement

labarai