Connect with us

LABARAI

Cikin Kwana Guda Mutum 69 Sun Kamu Da Korona A Bauchi

Published

on

Akalla mutane sittin da tara (69) ne suka kamu da cutar Korona a jihar Bauchi a cikin kwana guda.

Alkaluman da suka fito daga hukumomin lafiya a daren jiya Talata na tabbatar da adadi mafi tsoka da suka kamu da cutar a tarihin annobar Korona a jihar ta Bauchi.

Bayanin wadda yake kunshe a rahoton kullum da ma’aikatar lafiya ta jihar ke fitarwa domin shaida wa jama’a halin da ake ciki, bayanin ya nuna cewa an gudanar da gwajin tare da tabbatar da adadin masu dauke da cutar ne a dakin gwaje-gwajen cutuka da ke Bauchi.

A kan wannan matakin, kawo yanzu haka jihar Bauchi tana da mutum 131 da suke kan jinyar cutar a daidai lokacin da muke ciki.

Rahoton na cewa; “Ya zuwa yau Talata, 9 ga watan Yuni 2020, mun samu adadin wadanda suka kamu da cutar mafi yawa a tarihin wannan annoba a jihar Bauchi.

Ma’aikatar lafiya ta jihar ta shaida cewar kawo jiya Talata mutum 364 aka tabbatar sun kamu da cutar tare da sallamar wasu ba’adin da suka warke, sai kuma mutum 131 da yanzu haka suke jinyar cutar a kwance a cibiyar killacewa, “Zuwa yanzu, mun dauki samfurin mutum 2,478 tun bayan barkewar cutar a jihar, bincike ya tabbatar da cewar mutum 364 ne suka kamu da cutar a jihar Bauchi, amma tunin muka sallami mutum 224 bayan sun warke daga cutar.”
Advertisement

labarai