Cin Hancin Dala Miliyan 20: Gwamnatin Tarayya Za Ta Bi Kadi

Daga Wakilinmu  

Gwamantin tarayya na yin nazari ko kuma tunanin soke yarjejeniyar da Hukumar Tashar Jiragen Ruwa ta kasa ta kulla da wani kamfani na kasar Cyprus, sakamakon zargin cin hanci na Dalar Amurka miliyan Ashirin da ake zargin wasu jiga-jigan hukumar da samun hannunsu dumu-dumu.

Daukar matakin ya faru ne bayan wata uku da ofishin lauyan Kasar Swissa watan  Mayun shekarar 2017 ya saki rahotonsa, inda rahoton ya bayyana daya-bayan daya na badakalar cin hancin da ake zargin wasujami’an hukumar sun karba tsakanin shekarar 2007 zuwa shekarar  2011.Kimanin Dalar Amurka miliyan 18 ake zargin kamfann ya turo ga wasu kamfanonin Shell dake kasar nan.

Bugu da kari rohoton, kamfanin an ci tarar sa na miliyan daya na kudin kasar ta Swiss kuma aka umarce shi da ya dawo da miliyan 36 na kudin kasar ta Swiss, kuma aka danganta ribar da kamfanin ya samu a matsayin haramtacciya.Sakamakon bayar da wannan rahoton da mahukuntan kasar ta Swiss ta yi.

Babbar Hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, Hajiya Hadiza Bala Usman, kwanan baya ta bayyana cewa, kamfanin, Hukumar Hana cin Hanci da Rashawa (EFCC) zata hukunta kamfanin..

A cewar Hajiya Hadiza, hukumar ta samu izinin hakan ne daga kotun kasar ta Swiss, inda ta kuma turawa hukumar ta EFCC don gudanar da binciken, tare da bincikar jami’an da ake zargin sun amfana da cin hancin.Ta kara da cewa, Hukumar ta kuma tura ofishin Akawu na kasa takardun da kotun kasar Swiss ta turo akan zargin badakalar.

Jaridar LEADERSHIP A Yau ta sunsuno cewa, sake yin nazari akan kwangilar ko kuma soke ta gaba daya, ya zama wajibi a yanzu, idan aka yila’akari da binciken da ofishin Akawun gwamnatin tarayya ya gudanar.

Wasu daga cikin abubuwan da gwamnatin tarayya tayi la’akari dasu akan kamfanin, sun hada da sake yin nazari akan kwangilar da aka bai wa kamfanin sun hada da sanya wa kamfanin takunkumi da kuma hana shi duk wata harkar kasuwanci da Hukumar ta Jiragen Ruwa ta kasa da kuma sanya masa sababbin hukunce-hukunce da duk wani kamfani da zai yi harkar kasuwanci a kasar nan, tare da hukunta jami’an Hukumar ta tashar jiragen ruwan kasar nan da kuma tsofaffin ma’aikatar hukumar.

An kuma bayya cewar, Ofishin Akawun gwamnatin tarayya a bisa bincikenda ya gudanar, ya gano cewa, kamfanin yana daya daga cikin kamfanoninda aka kulla yarjejeniya dashi, inda kuma ya gudanar da aikinkwangilar ga Hukumar ta Tashoshin jaragen Ruwa ta kasa har ta sama daNaira biliyan bakwai da sha hudu a wasu shekaru da suka shige.

Har ila yau, an bankado cewa, tsofaffin  jami’an Hukumar ta tashashenjiragen ruwan, suna daga cikin wadanda suka amfana da badakalar, ammasai dai, rahoton kasar bai ta ambato sunansu ba.

Kamfanin dai, ya shiga yarjejeniya da hukumar ne, a shekarar 2005, donkafa yadda za a kawo saukin yin fito ga dukkan masu amfani da jiragenruwa dake tsibirin yammacin Bonny Onne, da  Okrika kuma Fatakwal. Hukumar ta jiragen ruwa ta kasa tana da kashi sittin bisa dari, indakuma hukumar BonnyChannelManagement za ta dauki kashi arba’in bisa dari.

Wata majiya a hukumar ta jiragen ruwan kasar nan, da ba ta so a bayyanasunanta ba, ta shedawa jaridar LEADERSHIP cewa, kamfanin da akezargin ya amsa zargin da ake masa na bada cin hancin ga wasu jami’anhukumar sai dai, sun bada cin hancin ne saboda jami’an sun ki basurasidansu.

A bangaren kamfanin a wata takarda da ya gabatar wa da Hukumar jiragenruwan ta kasa ya ce, ya shinfida wasu matakai don magance irin hakannan gaba, duk da cewar kamfanin ya kuma biya tarar da mahukunta kasarSwiss taci tarar shi.

Wata majiya ta shedawa jaridar LEADERSHIP A Yau cewa, kudurin gwamnatin tarayya na soke yarjejeniya yanadaga cikin yunkurin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na kakkabe cin hanci da rashawa a kasar nan.

Majiyar ta kara da cewa, uzurin da kamfanin ya bayar na dadin bada cinhancin bai da wata madafa.Hukumar ta tashoshin jiragen ruwa ta bayyana cewa, ta nemi shawarar

lauyoyin ta da sauran masu ruwa da tsaki akan maganar.Tuni dai, hukumomin yaki da cin hanci daban-daban, suka fara bincike akan badakalar.

An ruwaito wata majiya tace, za a sanar da ‘yan kasa, akan samakon binciken zargin badakalar. Bugu da kari, an ruwaito wata majiyar tace, hukumar tashoshin jiragen ruwa ta kasa, a tsaye take don kawo karshen cin hanci da rashawa ahukumar ta hanyar gwamnatin tarayya.

Exit mobile version