Cin Zarafin Maigadi: Manyan Lauyoyin Ƙasa Na Neman A Dakatar Da Alƙali Danladi Umar

Daga Sulaiman Ibrahim

Kwana uku kenan, bayan da shugaban Kotun Tarbiyya ‘Code of Conduct Tribunal (CCT)’, Mista Danladi Umar, yaci zarafin wani mai gadi a wata babbar flaza a Abuja.

Lamarin yabar baya da kura, yadda tuni wasu manyan lauyoyi da kungiyoyin farar hula masu rajin kare hakkin Dan Adam ta kasa suka fara kira ga gwamnati da adakatar da shugaban kotun CCT, Danladi Umar.

A cewarsu, ya kamata a gabatar da koke ga Majalisar Shari’a ta Kasa (NJC) da Ofishin Babban Lauyan Tarayya don daukar matakin da ya dace.

Wasu manyan masu fada a ji wadanda suka zanta da Jaridar LEADERSHIP sun ce ya dace masu rike da mukaman gwamnati su kame kansu ta hanyar da ta dace.

Sun kara da cewa, bai kamata Wanda ke rike da mukami yayi amfani dashi don cin zarafin na kasa dashi.

Daga cikin manyan Lauyoyi da masu rajin kare hakkin dan Adam da suka nemi a hukunta Mista Danladi Umar Sun Hada da:

Cif Awa Kalu, Cif Mike Ahamba, Malam Abdul Balogun, Farfesa Ernest Maduabuchi Ojukwu, Kunle Adegoke

Daga cikin shugabanni masu rajin kare hakkin dan Adam sun hada da:

Sugaban tsare-tsare na harkokin cigaban gwamnati, Ibrahim Faruk, Darekta ta cibiyar cigaban ‘yancin Dan Adam Idayat Hassan, Mai kira ga kyakkyawan tsarin gwamnati na Afirka, Jubril Momodu.

Exit mobile version