Yayin da cire tallafin man fetur ke ci gaba da kawo cikas ga rayuwar ‘yan Nijeriya, mazauna babban birnin tarayya Abuja sun ce akwai bukatar gwamnati ta kara duba yanayin da suke ciki.
Mazauna garin sun bayyana haka ne a wata hira da suka yi da kafofin yada labaran Nijeriya a Abuja ranar Lahadi.
- Cire Tallafin Fetur: Gwamna Makinde Ya Yi Wa Ma’aikata Karin Naira N25,000 Kan Albashinsu.
- Radadin Cire Tallafin Man Fetur: Kwan-gaba Kwan-baya Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar Kwadago
Wasu mazauna yankin sun ce galibin kudaden shigar da suke samu ana kashe su ne wajen siyan mai, wanda hakan ya sa su ke rike ragowar ‘yan kudade kadan don biyan wasu bukatu.
LEADERSHIP HAUSA ta rawaito cewa, Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu yayin da yake gabatar da jawabinsa a taron rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasa.
Bayan da shugaban ya bayyana haka, farashin man fetur ya tashi daga N195 a kowace lita, kuma a halin yanzu ana sayar da shi tsakanin N637 zuwa N660.
Ganin farashin man fetur din na kwanan nan na Oktoba 2023 da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar ta ce matsakaicin farashin litar man fetur ya karu daga N195.29 a watan Oktoban 2022 zuwa N630.63 a watan Oktoban 2023.
NBS ta ce, farashin N630.63 na watan Oktoba na shekarar 2023 ya nuna karin kashi 222.92 cikin dari na N195.29 a watan Oktobar 2022.
Karin farashin man fetur din ya haifar da tashin gwauron zabin kayayyakin abinci da sufuri da sauran kayayyaki fadin kasar.
Joanna Madu, wata ma’aikaciyar gwamnati ce da ta ce, cire tallafin na cinye mafi yawan albashin da take karba wanda ya gaza biya mata bukatunta da dama, inda ta bayyana lamarin a matsayin mai tsanani.