Akalla ‘yan jarida 10 ne suka samu tallafin kudi don gudanar da bincike kan cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma.
Cibiyar Fasaha da Ci Gaban Al’umma (CITAD) ce ta ba da tallafin tare da hadin gwiwar gidauniyar MacArthur.
- Miyetti Allah Ta Maka Gwamna Ortom A Kotu Kan Kwace Wuraren Yin Kiwo A Jihar Benuwai
- Daga Soyayyar Wata Yarinya Na Fara Waka —Abba Ganga
Babban Daraktan Cibiyar, Malam Yunusa Ya’u, wanda Buhari Abba ya wakilta, ya bayyana cewa tun farkon watan Yuni, CITAD ta bukaci ‘yan jarida da suka halarci taron bita na kwana biyu a jihar Bauchi, kan karamin tallafin bincike na yaki da cin hanci da rashawa.
Akalla mutane 15 ne suka shiga takarar neman tallafin.
Bayan da alkalai da masu ruwa da tsaki suka tantance, sun zabo ‘yan jarida 10 don ba su tallafin da za su yi amfani da shi wajen gudanar da bincike.
Babban Darakta na CITAD, Injiniya Y. Z. Ya’u, ya ce, tallafin wani hadin guiwa ne Gidauniyar Macarthur don bai wa ’yan jarida kwarin guiwa wajen yin bincike da kuma bayar da rahoton ayyukan cin hanci da rashawa a cikin al’umma ta hanyar jan hankalin gwamnati da masu ruwa da tsaki don yin gyara.
“CITAD ta dade tana aiki tare da ‘yan jarida don tabbatar da gaskiya da rikon amana a tsakanin jama’a kuma wannan tallafin zai zama na musamman duba da yanayin wadanda zasu yi binciken matasa ne masu sha’awar kawo canji a cikin al’umma.”
“Binciken ayyukan cin hanci da rashawa a cikin cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu zai inganta rayuwar jama’a musamman a cikin al’ummomin da ba su da murya don yaki da cin hancin.”
Wadanda suka yi nasara sun fito ne daga kafofin yada labarai daban-daban wadanda suka hada da:
1 – Auta Polycarp – Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).
2 – Ismail Auwal Garba – Sahelian Times.
3 – Edwin Philip – Breeze FM Lafia, Nasarawa.
4 – Anibe Idajili – TheCable.
5 – Hauwa Kabir Lawal – Daily Reality Newspaper, Jihar Filato.
6 – Abbakar Muhammad Usman – Daily Trust.
7 – Rabiu Musa – Hot Pen, Kano.
8 – Abdulhafiz Sultan – Jasawa Times, Jihar Filato.
9 – Muhammad Auwal Ibrahim – Wikki Times, Jihar Gombe.
10 – Zaharaddeen S. Yakubu – Daily Trust, Jihar Kano.