A ran 25 ga wata, an gudanar da tattaunawa kan “Zurfafa gyare-gyare a Sin dama ce ga duniya” a cibiyar al’adun kasar Sin dake birnin Abuja a Najeriya, wanda rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG da cibiyar raya al’adu ta kasar Sin suka shirya. Taron ya jawo manyan baki da masana wadanda suka gabatar da fahimta mai zurfi game da gyare-gyaren da kasar Sin ke yi da kuma tasirinsu a duniya.
An bude taron ne da jawabin mataimakin ministan yada manufofin JKS, kuma shugaban CMG Mista Shen Haixiong, inda ya jaddada muhimmancin ci gaba da yin hadin gwiwa tare da nuna godiya ga mahalarta taron.
- Masana Sun Bayyana Alfanun Manufar Gyare-gyaren Kasar Sin A Sabon Zamani A Abuja
- Sin Ta Shawarci Kasashen Da Suka Mallaki Makaman Nukiliya Kada Su Yi Amfani Da Shi Wajen Kaiwa Juna Hari
Muhimman jawabai sun hada da bayani mai zurfi kan tasirin kasar Sin ga tattalin arzikin duniya, da muhimmiyar gudummawar da take bayarwa ga yanayin tattalin arzikin Najeriya daga bakin malama Fa’iza Mustapha. Yayin da Misis Patricia Naria, wacce ta wakilci mai girma ministan ma’aikatar yawon bude ido ta tarayya Najeriya, ta mayar da hankali kan bunkasa harkokin yawon bude ido a Najeriya da karfafa gwiwar matasa domin dakile kaura daga karkara zuwa birane.
Taron ya kasance dandalin tattaunawa da mu’amala mai karfi, inda ya bayyana irin gyare-gyaren da kasar Sin ke aiwatarwa, da tasirinsu a duniya, wanda ya nuna muhimmancin ci gaba da yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Najeriya, wajen cimma muradun ci gaba na bai daya.
Bugu da kari, a ranar 24 ga watan Yuli agogon kasar Afirka ta Kudu, CMG ta gudanar da irin wannan taro a birnin Johannesburg, inda shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.
Shen Haixiong ya bayyana cewa, kwanan nan aka yi nasarar kammala cikakken zama karo na uku na kwamitin kolin JKS karo na 20 a birnin Beijing, wanda ya jawo hankalin duniya baki daya.
Wannan wani gagarumin ci gaba ne ga kasar Sin a sabon zamani. CMG ya himmatu wajen ba da labaran gyare-gyaren kasar Sin da bude kofa ga waje, da ba da labaran zamanantarwa irin ta kasar Sin, da yin aiki tukuru wajen gina gada ta cudanya da mu’amala, da tattaunawa, da fahimtar juna, da tuntubar juna tsakanin Sin da kasashen duniya.
Kazalika a wannan rana, CMG ya yi nasarar gudanar da taron tattaunawar a birnin Lusaka na kasar Zambiya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)