A yayin bikin “Ranar Muhalli ta Duniya” da aka yi a yau Lahadi, an kaddamar da “Aikin kafofin watsa labarai na kare muhalli na Sin da Afirka” a hukumance, wanda sashen babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG dake nahiyar Afirka ya kaddamar a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.
A yayin bikin kaddamar da aikin, CMG da muhimman kafofin watsa labaru na wasu kasashen Afirka da dama, sun gabatar da shawarar “Yin murya domin muhallin halittu” tare, inda aka yi kira ga kafofin watsa labaru na kasar Sin da na Afirka da su hada karfi don inganta mu’amala da koyi da juna a tsakanin jama’a kan ra’ayoyi da ayyukan kare muhalli.
Wakilai sama da 30 daga kungiyoyin kasa da kasa kamar UNEP, UNDP, UNICEF, da WWF, wakilan shugabannin siyasa daga kasashen Afirka, jami’an hukumomin kare muhalli, da wakilan manyan kafofin yada labarai daga kasashen Afirka da dama ne suka halarci bikin kaddamar da aikin.
Susan Gardner, darektar sashen kula da muhalli na UNEP, ta ce kafafen yada labarai na iya “jawo hankalin jama’a kan al’amurran muhalli da aka yi watsi da su, tare da gabatar da hujjoji ba tare da nuna banbanci ba ga jama’a”.
Shugaban kasar Seychelles, Wavel Ramkalawan, yayi imanin cewa, wajibi ne kafofin watsa labaru su fadakar da bil’adama su gane cewa, dukkanmu iyali guda ne, kuma makomar mu na zama irin ta bai daya ne. Kaddamar da wannan aikin, ya nuna muhimmancin hadin gwiwar kafofin watsa labaru na Sin da Afirka.
Ministan yawon bude ido na kasar Kenya Najib Balala ya bayyana cewa, yin magana da murya guda karkashin hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaru na kasar Sin da na Afirka zai iya yin tasiri wajen fadakar da mutane masu yawa da su rungumi ayyukan dake shafar kiyayewa da kuma gyara duniyarmu.
Jawo hankalin jama’a na da matukar muhimmanci ga shirin kare muhalli.
A nasa bangaren, Yakubu Mohamed, shugaban gidan talabijin na kasa a Najeriya, ya ce akwai fa’ida ta musamman da kafafen yada labarai ke da su wajen janyo hankalin jama’a don su maida hankali kan batutuwan da suka shafi kiyaye muhalli. (Mai fassara: Bilkisu Xin)