An kaddamar da bikin mu’amalar al’adu da jama’a mai taken “Amsa kuwwar zaman lafiya” wato “Echoes of Peace” a daren ranar 13 ga wata, a hedkwatar MDD dake birnin New York. An kaddamar da bikin ne bisa hadin gwiwar babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG da zaunanniyar tawagar wakilan kasar Sin dake MDD, inda shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. A sa’i daya kuma, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Fu Cong da mataimakiyar babban magatakardan MDD Melissa Fleming sun halarci bikin tare da gabatar da jawabai, lamarin da ya kaddamar da bukukuwan mu’amalar al’adu da jama’a na CMG mai taken “Echoes of Peace” a kasa da kasa.
Cikin jawabinsa, malam Shen Haixiong ya bayyana cewa, a bana ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin kin jinin harin sojojin Japan, da yakin kin tafarkin murdiya. Kuma cikin bikin na wannan karo, za a iya kallon fina-finan kasar Sin kamar “Flying Tigers” da “The Sinking of the Lisbon Maru” da dai sauransu, ta yadda jama’ar kasa da kasa za su kara fahimtar darajar zaman lafiya, da kara hada kai wajen kiyaye zaman lafiya.
Haka kuma, CMG zai ba da jerin rahotannin bukukuwa ta dandaloli da harsuna daban daban, domin kara wayar da kan jama’a kan gaskiyar batun da tarihin yakin duniya na biyu, ta yadda za a karfafa yanayin adalci a nan duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp