ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Collins Whitworth Zai Kafa Tarihin Shiga Kundin ‘Guinness World Record’ Tare Da Goyon Bayan Indomie

by Leadership Hausa
3 months ago
Indomie

A ranar 1 ga Oktoba, 2025, Collins Whitworth, ɗalibi a Jami’ar Bayero Kano (BUK), zai yi ƙoƙarin kafa tarihi a ƙoƙarinsa na karya karɓe kambun ‘Guinness’ na Duniya guda biyu a fannin fasahar zanen fuska: zanen fuska mai yawa cikin minti 3, da kuma fuska tarin yawa a cikin awa 1.

Yana ƙoƙarin karɓe kambun nasara daga Emilia Zakonnova da take riƙe da shi, wadda ta zana fuskar mutane 12 cikin minti 3, a ranar 30 ga Yuli, 2025. Wannan yunƙurin ba kawai nasarar Collins ba ce kaɗai, har ma ga ‘yan baiwa masu fasahar ƙirƙira a Nijeriya da matasa masu burin cimma burinsu na rayuwa.

  • An Kwace Kambun Hilda Baci A Gasar Dafa Abinci Ta Duniya
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano

Rayuwar Collins cike take da juriya da zuciyar jajircewa da ƙudure-ƙudure. Ko da yake ƙoƙarinsa na 2024 bai kai ga yin nasara ba, amma hakan ya ƙara masa ƙwazo da himma sosai, inda a yanzu ya dawo da ƙarfinsa. A cikin shekarar da ta gabata, ya sadaukar da awanni da yawa wajen ƙwarewa, daidaita sauri da yin tunani mai zurfi domin ya yi nasarar kafa tarihi.

ADVERTISEMENT

“Na koyi abubuwa da yawa daga yunƙurina na farko. A wannan karon na yi shirye-shirye na musanman tare da mayar da hankali da kuma ƙudurin yin nasara tare da goyon bayan Indomie, na yi imani za mu kafa tarihi tare,” in ji Collins.

Zanen fuska, ko da yake ana ganinsa a matsayin nishaɗi, fasaha ce mai ɗauke da ƙwarewa da take buƙatar ƙirƙira da kuzari ko saurin hannu. A wajen Collins, kowace fuska da ya zana tana bayyana wani saƙo tare da al’ada da kuma sanya farin ciki ga waɗanda suke sha’awar fasahar zane-zanensa. Yunƙurinsa na karɓe kambun tarihi na Kundin Guinness yana nuna yadda fasahar take da tasiri amma ba a bai wa ɓangaren dama sosai ba, yana haskaka yadda matasan Nijeriya su yi fice a duniya.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ake Funkason Fulawa

Yadda Ake Yin Pizza A Gida

Indomie, a matsayin jigo da ta daɗe wajen nasarar samar da abinci mai gina jiki ga al’umma, tana alfahari da tallafawa wannan yunƙuri na kafa tarihi na Collins. Shekaru da dama, Indomie ta tallafa wa shirye-shiryen tallafawa a fannin ƙirƙira da ilimi da sana’o’i ga matasa. Tallafawa Collins, wata alamar nasara ce da take nuna ƙoƙarin Indomie na isar da saƙo mai ƙarfi ga jama’a wajen cimma manyan burika da muradan rayuwa da suke bukatar samun goyon baya da ƙarfafa guiwa.

Shigar cikin wannan al’amari wata babbar alama ce da take tabbatar da cewa wannan taron na tarihi ya sami haske da karramawa kamar yadda ya dace, taro ne da yake ƙarfafa wa matasan Nijeriya guiwa domin su samu nasarar cimma burinsu na rayuwa ta hanyar samun ƙwarin guiwa.

An tsara taron zai gudana a Kano a Ranar samun ‘yancin mulkin ƙasa Nijeriya, inda ake sa ran jama’a da iyalai da ɗalibai da masoya fasaha da ƙirƙira da ‘yan jarida daga ko’ina a cikin ƙasa za su hallarci taron. Masu kallo za su samu damar shaida tarihin da Collins zai kafa a lokaci wajen zana fuskar mutane sama da 12 a cikin minti 3 da kuma zana fuskar mutane fiye da 220 cikin awa 1.

Wannan taro da zai samu halartar jama’a zai bunƙasa al’ada da ƙirƙira kuma zai sa ranar ta kasance ta musanman ba kawai taro kadai ba, inda ranar za ta zama muhimmiyar ranar biki ta baje-kolin nuna baiwa da samar da haɗin kai.

Ƙoƙarin kafa wannan wannan tarihin da karbe kambun zai samu goyon baya da bai wa matasa dama ta musanman. Labarin Collins zai ja hankalin matasan Nijeriya waɗanda suke da mafarkin samun shahara a duniya. Kuma zai zama wata shaida ta cimma ƙuduri bayan samun dama da ƙarfafa guiwa daga Indomie a ɓangaren fasaha a Nijeriya.

A yayin da Kano ke shirin karɓar baƙi domin gudanar da wannan gagarumin biki a wannan rana mai ɗumbin tarihi, jama’a na cike da farin ciki a harabar jami’ar da kafafen sada zumunta da wurare daban-daban. Yunƙurin Collins ba kawai nasara ce ta ƙashin kansa ba; lokaci ne na tarihi wanda ke nuna ci gaban fasahar ƙirƙira a Nijeriya a idon duniya, kuma wata ‘yar manuniya ce da take nunawa kowa cewa samun manyan nasarori na farawa ne da sha’awa da ƙuduri da kuma samun tallafi.

Taken Indomie na “Mafarki mai yawa na haifar da nasarori masu yawa” an sanya shi a cikin muradin Collins. A ranar 1 ga Oktoba, duk idanu za su koma Kano domin ganin Collins Whitworth yadda zai kafa tarihi, ba kawai ta zanen fuska ba, har ma ta bayyana irin ƙwazonsa da baiwarsa da yadda zai zama abin alfahari ga ƙasa Nijeriya. Wannan taron wani muhimmin taro ne a duk faɗin Nijeriya a ɓangaren fasaha tare da ƙarfafa guiwar matasa wajen cikar muradan su.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Ake Funkason Fulawa
Girke-Girke

Yadda Ake Funkason Fulawa

December 20, 2025
Yadda Ake Yin Pizza A Gida
Girke-Girke

Yadda Ake Yin Pizza A Gida

December 14, 2025
Yadda Ake Yin Pizza A Gida
Girke-Girke

Yadda Ake Yin Pizza A Gida

December 7, 2025
Next Post
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Da Gonaki A Kogi, Ta Tsaida Aiyuka A Legas

Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Da Gonaki A Kogi, Ta Tsaida Aiyuka A Legas

LABARAI MASU NASABA

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.