Connect with us

LABARAI

Compol Gombe Ya Kai Ziyarar Neman Hadin Kai Hedikwatar Tsaro Ta NSCDC

Published

on

Sabon Kwamishinan Yan sandan jihar Gombe da ya kama aiki kimanin mako biyu a jihar Maikudi Ahmed Shehu, ya kai ziyarar neman hadin kai wa kwamandar hukumar tsaron farin kaya ta NSCDC ta jihar Altine Sani Umar a helkwatar hukumar.

Kwamishina Maikudi  Shehu, yace a matsayin sa na Sabon Kwamishinan Yan sanda a jihar ne da yake son kawo sauyi ne ya sa ya kai ziyarar dan ganawa da takwarar sa ta cibil depence dan suyi aiki tare.

Batun hakan yana dauke ne a cikin wata takarda mai dauke da sanya hannun Jami’in hulda da jama’a na helkwatar  hukumar ta NSCDC dake Gombe Buhari Sa’ad da ya aikewa manema labarai

Ya ce, idan suka hada kai da juna dan yin aiki tare za su iya kawo karshen duk wata matsala ta tsaro da ta addabi jihar.

Da ta ke karbar Sabon Kwamishinan a helkwatar hukumar na NSCDC Kwamandar hukumar ta jihar  Gombe Hajiya Altine Sani Umar, bayyana cewa tayi hukumar ta a kullum a shirye take ta ba shi hadin kan da ya kamata  dan suyi aiki tare su shawo kan matsalar tsaro a jihar.

Altine Sani Umar,ta kuma ce hukumar NSCDC, ba za ta yi kasa a guiwa ba kamar yadda ta saba na ci gaba aikin da suke yi na yaki da batagari a sassan jihar wanda hakan yasa jama’a suke jinjina mu su.

Daga nan sai Altine Sani Umar, ta tabbatar wa da Kwamishinan yan sanda cewa a duk lokacin da ya nemeta dan suyi aiki tare kofar ta a bude take dan bada  gudumawar da suka saba domin hukumar cibil depence a Gombe suna taka rawar gani sosai a bangaren samar da tsaro.
Advertisement

labarai