Coutinho Ya Koma Barcelona Daga Liverpool

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Philippe Coutinho ya koma Barcelona kan kudi fam miliyan 142, bayan da dan kwallon bai bi Liberpool wasan atisaye da ta je yi a Dubai ba.

Coutinho ya zama dan kwallo na biyu da aka saya mafi tsada a duniya, bayan Neymar da ya koma Paris St Germain daga Barcelona kan kudi fam miliyan 200 a kasuwar siye da siyar day an wasa ta bana.

Liverpool ba ta sallama tayi uku da Barcelona ta yi wa Coutinho ba a kwanakin baya sannan ba ta bai wa dan wasan izinin barin kungiyar ba kamar yadda ya bukata kafin a fara kakar shekarar nan.

Tayin kudi na karshe da Barcelona ta yi wa Coutinho shi ne fam miliyan 118 tun kafin a fara kakar wasanni ta bana sai dai duk da haka kungiyar ta kasar ingila bata amince da cikin ba

Coutinho bai bi Liberpool atisayen da ta je Dubai ba, sakamakon jinyar raunin da yake yi, kuma bai buga wa kungiyar wasa biyu da ta buga ba.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dai tana zawarcin dan wasanne wanda take tunanin zai maye gurbin Neymar wanda yabar kungiyar a watan Agustan daya.

 

Exit mobile version