Coutinho Zai Sake Komawa Ingila

Rahotanni da ke fitowa sun nuna cewa dan wasan tsakiya na kungiyar Barcelona da yiwuwar ya tashi daga kungiyar ya koma Ingila da buga wasa.

Wata majiya ta kusa da Philippe Coutinho na Barcelona, ta ce dan wasan na shirin barin gasar La Liga zuwa ta Firimiyar Ingila, gasar da ya bari, bayan rabuwa da tsohuwar kungiyarsa ta Liverpool.

Rahotanni sun ce tuni wakilan Coutinho, Kia Joorabchian da Giuliano Bertoluci, suka tuntubi kungiyoyin Manchester United da Chelsea dangane da yiwuwar komawar dan wasan zuwa daya daga cikinsu.

A makon nan kuma ake sa ran kungiyoyin da Coutinho ya tuntuba za su bayyana matsayarsu kan bukatar.

Exit mobile version