Abubakar Abba" />

Covid-19: Bankunan Nijeriya Na Cikin Hatsari Sakamakon Faduwar Farashin Mai – Fitch Ratings

A jiya ne, kungiyar bayar da rance na kasa da kasa wacce ofishinta ke garin New York da London mai suna Fitch Ratings ta bayyana cewa, bankunan Nijeriya za su shiga cikin hatsari, sakamakon faduwar farashin mai a kasuwan duniya saboda annobar Coronabirus. Kungiyar ta daina bayar da bashin kadara sakamakon babban barasanar da bangaran albarkatun mai da gas ke kara samu. Ta bayyana cewa, kasashen duniya da yawa suna cikin tsari sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya, musammam ma a wannan lokaci da Nijeriya ke samun kadaden shiga na kashe 95 daga man da take fitarwa a kasashen duniya wanda da shi take inganta tattalin arzikinta.

A cewar kungiyar, faduwar farashin mai zai sa kudade su rage daraja. Kungiyar ta kara da cewa, faduwar farashin mai a kasuwan duniya, makaramar koma baya za a samu ba a tattalin arzikin duniya. Ta ci gaba da cewa, wannan annoba ya haifar da matsala ga tattalin ariki a kasuwannin duniya kuma ya sa jefar masu amsar bashi cikin rashin tabbas. Kungiyar ta bayyana cewa, “muna kira ga babban bankin Nijeriya (CBN) da masu hannu da shuni da su taimaka wa wasu kasuwanci da basukan kudade domin bunkasa tattalin arikin kasar. Wannan zai taimaka wajen shawo matsalar matsin tattalin arzikin da za a fuskanta sakamakon faduwar farashin mai a kasuwannin duniya saboda wannan cuta ta Coronabirus. A kwanan nan ne bankuna guda uku a Nijeriya suka shiga cikin matsi sakamakon bashi ya musu katutu, yayin da bankuna 10 ne kacal ba a bin su bash, bankuna a Nijeriya za su fada cikin garari a watan da za a shiga nan gaba sakamakon wannan bala’i. Yana da matukar mahimmanci a samar da hanyoyin da za a bunkasa tattalin arziki bayan wucewar wannan cuta. “Kamfanonin mai da gas da ke wakiltar bankunan Nijeriya yana tattare da tulin bashi wanda ya kai na kashi 30 tun farkon watanni shida ta shekarar 2019. Wannan lamari yana da dangantaka ne da faduwar farashin mai a kasuwan duniya wanda ya yi dai-dai da faduwar farashin mai a kasuwar duniya da aka taba samu a shekarar 2008-2009 da kuma shekarar 2015-2016. An dai samu saurin rage basussuka a shekarar 2017 lokacin da farashin mai ya yi goron zabi a kasuwannin duniya, amma wannan matsalar ta yanzu ta zarce duk inda ake tunani. A yanzu bangaren man fetun a kasuwannin duniya yana fama da matsala, sakamakon farashin mai da ya fadi warwas a kasuwannin duniya,” in ji Fitch.

Exit mobile version