El-Zaharadeen Umar, " />

Covid-19: Ka Maida Mu Saniyar Ware – Kwararun Ma’aikatan Lafiya Ga Masari

Gamayyara ma’aikatan lafiya a jihar Katsina sun koka akan yadda gwamnatin jihar Katsina ta maida su saniyar ware a cigaba da lalubu hanyoyin magance bullar cutar mashako da ta sanya duniya gaba.

Dakta Mouhammad Nafi’u Abdul’azizi ya bayyana haka a lokacin wata zantawa da ya yi da manema labarai a Katsina, jim kadan bayan kammala wani taro da suka yi akan wannan batu da ya addibi al’umma da kuma duniya baki daya.

Dakta Mouhammad Nafi’u ya kara da cewa hanyoyin da gwamnatin jihar Katsina ta dauko na yaki da wannan cuta abin a yaba ne, sai dai kwamitoci guda biyu da aka kafa babu kwararun ma’aikatan lafiya a ciki wanda kuma hakan yana iya shafar nasara da ake bukata.

Daga cikin shawarar da suka cimmawa a lokacin taron na su, sun hada da kira ga gwamnati da ta kara matsa kaimi akan rufe kan iyakoki da ta yi sannan ta samar da isasun kayan aikin akan iyakokinta da sauran jahohi da kuma jamhuriyar Nijar.

Haka kuma suna bada shawara ga gwamnatin jihar Katsina da ta hada hannu da hukumar kula da cututuka ta kasa wato NCDC domin samar da dakin gwajin anan Katsina saboda a saukaka zuwa Abuja ko Lages

Kazalika kungiyar ta bada shawarar cewa lallai a samar da wuri na musamman a matsayin wuraren kibe jama’a wadanda ake zargin suna dauke da wannan cuta, ba kamar yadda gwamnatin ga gwama wadannan wurare a cikin asibitoci ba, inda suka wannan babu kwarewa acikin  aikin kiwon lafiya, saboda haka suna ganin a yi amfani da Katsina City Mall da kuma IDP Camps a matsayin wurare na musmman

“Muna bukatar isason kayan aiki domin bada kariya ga ma’aikatan lafiya, da suka hada da safar hannu, abin rufe fuska da rigar kariya da hula da sinadarin wanke hannu domin ta haka ne ma’aikatan lafiya za su iya kare kansu daga wannan cuta kafin su kare marar lafiya” inji kungiyar

Kungiyar ta ce duk da anki sanya mambobinta akan wannan muhimmin aiki ba zata yi kasa a gwiwa ba wajan ganin ta bada tata gudunmawa wajan wayar da kan jama’a musamman na karkara ta hanyar amfanin da kafafen yada labarai domin sanin hanyoyin da za su kare kansu daga kamuwa da wannan cuta ta Cobid 19

Dakta Mouhammad Nafi’u ya kara da cewa babu bullar wannan cuta a jihar Katsina amma hanyoyin da kawai za a iya amfani da su wajan kare kai su ne, abubuwan da gwamnati ta dauko hanyar yi, wanda ya ce suna fatan za a ga kwararun aciki domin samun nasarar da ake bukata.

Haka kuma sun nuna matukar farin cikinsu akan yadda wasu mutane suka fara bada gudunmawa domin yakar wannan cuta inda suka yi kira ga sauran da su taimaka da abinda suke da shi domin a gudu tare a tsira tare.

Daga karshe sun yi kira ga al’ummar jihar Katsina baki daya da masu rike da masarautun gargajiya da malaman addini da su kasance masu bin doka da oda musamnnan sharudan da gwamnati ta gindaya akan abinda ya shafi bullar wannan cuta.

 

Exit mobile version