Manoman Tumatir a Jihar Kano, na ci gaba da fuskantar barkewar annobar cutar da ke lalata Tumatirin da suka shuka.
Cutar, wadda a turance ake kira da ‘Tuta Absoluta’, ta shafe shekaru tana lalata gonakin da aka shuka Tumatir.
- Kwararru Sun Yi Musayar Ra’ayoyi Dangane Da Wayewar Kan Sin Da Afirka
- Kasar Sin Ta Mallaki Tasoshin Fasahar 5G Miliyan 4.4 A Halin Yanzu
Duk da kokarin da cibiyoyin bincike kan amfanin gona ke yi, wadanda suka hada da cibiyar binciken ‘ya’ayan itatuwa da ke garin Ibadan a Jihar Oyo, wannan cuta ta faskara samun magani.
Kazalika, duk binciken da kungiyoyin kasashen waje masu bayar da dauki na kawo karshen cutar, amma hakan ya gagari Kundila, duba da yadda cutar ta sake bulla a jihar.
Kungiyar manoman Tumatir ta kasa reshen Kano (TOGAN), karkashin jagorancin Alhaji Sani Danladi Yadakwari ta bayyana cewa, cutar ta kara barkewa a wasu gonakin manoman Tumatir a jihar.
A cewarsa, hakan ya kuma jawo lalata gonakin na Tumatirin da ke wasu sassan jihar.
Yadakwari ya kara da cewa, hakan ya tilastawa manoman Tumatir da dama a jihar dakatar da nomansa, duba da irin mummunar asarar da suka yi.
Ya ci gaba da cewa, manoman Tumatir da suka fara lura da barkewar cutar ce suka sanar da kungiyar, inda kuma kungiyar ta shigo cikin lamarin ta kuma gano cewa, cutar ce ta sake dawowa gonakin manoman na Tumatir.
A cewarsa, maoman Tumatir a jihar, sun shafe shekaru suna yin asara sakamakon barkewar cutar, wanda hakan ya sanya wa manoman rashin sha’awar ci gaba da noman nasa.
“Mun gano bullar annobar ce a wasu gonakin da aka shuka Tumatir a
Garun Malam, Kura, Bunkure, Bagwai da sauransu”, in ji Yadakwari.
Ya sanar da cewa, duba da ilimin da muke da shi kan cutar, mun yi zargin cewa, annobar ce ta sake dawo ga gonakin na noman Tumatir da ke jihar.
“A bangaren kungiyar, mun dauki matakan da suka dace tare da rubuta wasika zuwa ga ma’aikatar aikin gona ta jihar, domin sanar da su dawowar annobar, inda a yanzu muke ci gaba da jiran amsa daga wurinsu”, a cewar Yadakwari.
Wannan cuta dai, an gano bullarta ne a shekarar 2016, wadda kuma ta jawo lalata gonakin manoma da dama da ke jihar.
Bugu da kari, bayan sake dawowar cutar, an fara fuskantar karancin Tumatir a akasarin kasuwannin da ke jhar, wanda kuma hakan ya haifar da tashin farashinsa zuwa sama da Naira 75.
Kazalika, manomansa da hukumomin gwamnati, sun tashi tsaye wajen yakar wannan cuta, amma sai dai, har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp